(ABNA24.com) Bisa Bukatar mahukuntan kasar Saudiya Amurka ta tura dakarunta masu yawa da kayan yaki zuwa Saudiyar domin kalubalantar abin da suka kira barazanar kasashen Iran da Yemen.
Cikin wani rahoto da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar ta ce tunita tura dakaru dari biyar zuwa Saudiyya saboda abin da ta kira barazana da ke karuwa a yankin gabas ta tsakiya.
Ma'aikatar tsaron Saudiyya ma ta tabbatar da cewa Sarki Salman ya amince da matakin, domin inganta harakokin tsaro a yankin.
Rabon da kasarAmurka ta girke dakaru a Saudiyya tun 2003 a lokacin da suka fice bayan kammala yaki a Iraqi.
Wannan na zuwa a yayin da Birtaniya ta shawarci jiragen ruwanta su kauracewa mashigar Hormuz a tekun fasha bayan da Iran ta tsare jirginta na dakon mai.
Shugaba Trump na Amurka ya sha alwashin aiki kafada da kafada da Birtaniya bayan Iran da ta tsare jirgin ruwan nata.
/129
23 Yuli 2019 - 03:56
News ID: 963572

Bisa Bukatar mahukuntan kasar Saudiya Amurka ta tura dakarunta masu yawa da kayan yaki zuwa Saudiyar domin kalubalantar abin da suka kira barazanar kasashen Iran da Yemen.