Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBaiti: an gudanar da taron tunawa da wafatin Imam Khumaini (RA) da kuma girmama shahidan hidima bisa halartar Ayatullah Reza Ramezani babban sakataren majalisar Ahlul-baiti (AS) a gidan jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.
Ghadir, Abin Koyi Na Duniya Ga Wadanda Suka Cancanta
A yayin taron, Ayatullah Ramazani ya bayyana cewa, yayin da yake ishara da darussan Ghadir: Koyarwar Ghadir ita ce a dora wadandaa suka fi cancanta akan shugabanci. Duk wanda ya ke kwararre ne kuma mai kishin aiki ya kamata a dora gudanar da ikin, kuma a yau wannan koyarwar koyarwa ce ta duniya. Da a ce mafi kyawun mutane sun yi mulki a duniya, me zai faru a yau? Muna da Karbala guda uku, Karbala ta farko a shekarar 61, wanda muka yi magana da yawa game da dalilin da ya sa ta auku amma dangane da yanayin da ta faru ba mu magana dayawa ba. Ashura daya ce a cikin tarihi. Wasu suna cewa me yasa kuke ambaton Ashura. Ghazali yana da fatawa da ke cewa hramun ne kawo labarin Karbala, domin a karshe sai ka la'anci Yazidu, alhali kuwa Yazidu zai iya tuba kuma ta fuskar kyawawan halaye bai dace a la'ance wanda ya tuba ba. Wasu ma suna cewa Yazidu mujtahidi ne kuma ya yi kuskure. Wasu kuma sun ce Ashura wani abu ne na musamman kuma ba za a iya daukar ta a matsayin abin koyi ba.
Babban sakataren Majalisar Ahlulbaiti (AS) ya kara da cewa: Ashura ta uku ita ce ta Ashura da ta ke a hannunmu a yanzu. Idan yanzu ka na son binciko kalmar Ashura a harshen Latin, shafi na farko da zai fito shi ne zubar da jini da yanka. Lokacin da nake Vienna ina kallon wadannan, na yi matukar bakin ciki da yadda muka wulakanta Ashura. Yayin da Imam Khumaini (RA) yake cewa: Wallahi yin kukan Imam Husaini (RA) da Ashura siyasa ce, ma’ana yunkurin shugaban Shahidai (AS) shi ne ya kawo gyara ga al’umma, domin a zamaninsa an sake farfado da bidi’a, an kuma bata sunnoni.
Yayin da yake bayyana cewa Imam ya daukaka matsayin makarantun hauza, Ayatullah Ramezani ya jaddada cewa: Marigayi Imam ya ba da wata sabuwar ma'ana ga marja’iyya kuma ya ba mu girma da daukaka. A wani lokaci na je kasar Faransa na yi magana kan Imam Khumaini (RA), yawancin wadanda suka halarci taron ba Iraniyawa ba ne. Bayan jawabin, sai mutane da dama suka zo wurina suna cewa, Imam Khumaini (RA) ba na Iraniyawa ba ne kawai, marigayi Imam ajiyar Allah ne. Allah ya tanadi Imam Khumaini (RA) a wannan zamani ya rayar da mu da ruhinsa mai tsarki. Babu wanda ya san Imam Khumaini (RA), shahidi Motahari ya ce za’a iya sanin Allameh Tabatabaei a cikin wasu shekaru dari, tare da cewa sanin Imam Khumaini (RA) yana da bukata fiye da haka a kowane lokaci. Marigayi Imam ya kasance tushe kuma alama ce wacce ta cece mu kuma ta zurfafa da fadada hangen nesa ta yadda a yau za mu fahimci menene addini, Hajji, Ghadir da Ashura.
Imam Khumaini (RA); Mai Farfado Da Hukuma Da Martabar Al'ummar Musulmi
Yayin da yake ishara da mazhabar Imam Khumaini (RA) ya ce: Mu daliban wannan makaranta ne kuma wadanda suke yin koyi da wannan makaranta a kan wannan tafarki ba su da tsoron daukar kansu a matsayin bayin mutane. Daga cikinsu akwai shahidi Raisi da shahidi Amir Abdollahian. Shahidi Amir Abdollahian ya kasance wani abin koyi da ke nuni da ladabi a cikin tsarin diflomasiyya na Jamhuriyar Musulunci, kuma wannan shahidi a hakikanin ma'anar kalmar ya ba da wani sabon matsayi na tsarin diflomasiyya na Jamhuriyar Musulunci. Ina da alakar aiki da zuzzurfan tunani da wannan shahidi, kuma yana bayar da kulawa ta musamman ga Majalisar Ahlul Baiti (AS).
Babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: dukkan mu daliban makarantar Imam Khumaini (R.A) ne, yana da cikakken tsarin addini kuma ya yi imani da cewa kamata ya yi addini ya yi tasiri matuka ga dukkan bangarori. Imam Khumaini (R.A) ya ba wa musulmi marbata da kuma canza daidaiton duniya a fagen siyasa da addini. A da can kasashen Gabas da Yamma suna neman hannun jari, amma a yau abin da ya saba wa tsarin mulkin mallaka shi ne Musulunci da fahimtar Imam Khumaini (RA). Duk inda muka je a duniya suna son wannan fahimtar kuma suna bayyana soyayyarsu ga Imam Khumaini (RA). Jagoran ya taba cewa juyin juya halin Musulunci na Iran ba zai taba zuwa ko'ina a duniya ba ba tare da sunan Imam Khumaini (RA) ba. Don haka wajibi ne mu sake yin nazari tare da yin bincike kan rayuwar Imam Khumaini (RA) da tunani da hangen nesan sa, kada mu bari a juyar da tunanin marigayi Imam.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da ra'ayin Imam Khumaini (RA) kan Ghadir, Ayatullah Ramezani ya ce: Littattafai da yawa sun yi nuni da dalilin Ghadir, amma Imam ya gabatar da wata sabon ma’ana da tafsirin Ghadir. Ya ce Ghadir ya zo ne domin ya koya mana ydda zamu tabbata akan makomarmu. Dubi irin fassarar da ya yi wa Ghadir da kuma irin hangen nesa da yake da shi dangane da haka. Ghadir ya zo ne domin dan Adam ya samu rabo a rayuwarsa da makomarsa, don haka mutane suka yi mubaya'a ga Imam Ali (AS) na tsawon kwanaki uku a waki'ar Ghadir, ayarin da suka yi gaba suka komo baya domin yin mubaya'a.
Ya ci gaba da la’akarin cewa adalci da daidaito sun bambanta kuma ya fayyace cewa: Adalci shi ne adalcin zamantakewa kawai, amma cikakken adalci ya kasance ya hada da adalcin daidaikun mutane da adalci na zamantakewa. Allah ya umarci dan Adam da su kasance masu adalci da kyautatawa, kuma an dora mana alhakin tabbatar da adalci. Tabbas idan ana son adalci sai an biya farashi, don haka Imam Ali (AS) ya yi shahada a mihrabin sallarsa saboda tsananin adalci. Adalci yana daya daga cikin abubuwan da mutane da yawa suka kasa jurewa. A zamanin Imam Ali (AS) mun ga wasu mutanen da saboda tsammanin samun lada da sakamako yayin da aka zo managar adalci sai sukai kasa agwiwa.
Ya kara da cewa: Imam Khumaini (RA) ya so ya cusa mana tunanin cewa dole ne a dauki mataki a fagen tauhidi. Ba zai yiwu a kai matsayin tauhidi ba ba tare da mutunci ba. Yanzu haka a kasashen Yamma suma suna maganar mutunci, suna rera wadannan take har takai sun zalunci wadannan take. Ana zaluntar Adalci da ruhiyya a kasashen yamma. Turawan Yamma sun wulakanta ruhiyya har ta kai suna maganar samun ruhiyya ba tare da Allah ba kuma ba tare da addini ba. Sun kuma gurbata adalci shi ma. Turawan Yamma suna daukar adalci a matsayin misali: idan mutane biyu suna yaki, mu taimaki wanda ba shi da makami da ba shi makami domin su biyun su yi fada da juna da kyau. Ba wai neman sulhu da zaman lafiya suke yi ba, a’a suna neman su kunna kamfanonin sayar da makamai don samun riba. Daga cikin abubuwan da kasashen yammaci suka mayar da hankali a kai har da mutunci da daukaka, inda Turawan Yamma suka rage darajar daukaka da mutunci sosai. A lokacin tafiyata zuwa Senegal, na je tsibirin Goure, wanda aka fi sani da tsibirin Slave, kuma na tsawon shekaru ɗari uku wannan tsibirin wuri ne da ake ajiye bayi. Tawagogin da za su je can su ma dole ne su je tsibirin Goure don kada su shaku ko tausayawa da wadannan mutane.
Gudunmawar Imam Wajen Sake Fayyace Siyasa Da Addini A Karni A Yanzu
Haka nan kuma yayin da yake ishara da mahangar Imam Khumaini (RA) game da mutunci, Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: Fahimtar da marigayi Imam ya ba mu na addini ya sha bamban da sauran. Ya kasance yana cewa na zo ne domin in dawo maku da mulkinku da shugabancinku, na zo ne domin in mayar maku da girmanku, kuma a wannan harkar ina ganin kaina a matsayin bawa. Harkar Imam Khumaini (RA) yunkuri ne na annabta. Baya ga fagagen addini na daidaiku da na zamantakewa, Imam ya yi imani da cewa addini yana bukatar hukuma a lokacin da ake son aiwatar da shi a cikin al'umma. Ya yi imanin cewa ana bukatar gwamnati don samun adalci da mutunci. A mahangar Marigayi Imam, mulkin addini yana yiwuwa a zamanin da muke ciki da wannan zamani da zai zo nan gaba.
Haka nan kuma ya dauki sharadin tabbatar da adalci da aiwatar da dokokin shari'ar Musulunci a matsayin kafa gwamnati da wani shugaba mai adalci zai yi, ya kuma lura da cewa: Kafin nasarar juyin juya halin Musulunci wasu mutane sun yi imanin cewa kafa gwamnatin addini ba abu ne mai yuwuwa ba, don haka suka bayar da ra'ayin cewa babu wani juyin juya hali na addini da zai faru a duniya.., Amma Imam Khumaini (RA) ya jagoranci juyin addini ya kai ga nasara. A daidai wannan lokacin ne wasu mutanen birnin Kum da gidan yari, wadanda har ma aka daure su a gidan yarin, sun yi imani da yin gyara sannu a hankali, amma Imam Khumaini (RA) ya ce babu wani abu da za a iya yi tare da gyara sannu a hankali, kuma dole ne a yi juyin juya hali, don haka juyin juya halin addini ya faru, juyin juya hali wanda ya kasance mai tsarin tsarin addini na madaukaka tare da kusancin kara ingancin addini. Addini ba wai a wuraren Tahajjud ne kawai ba, da tsayuwar dare, da zubar hawaye, da ibada. Imam baya ga haka, ya fahimtar da mu cewa ibadar daidaiku ibada ce ta zamantakewa, don haka wajibi ne dan’adam ya tafi zuwa ga tsarin tauhidi, yayin da wadanda suka koma tafarkin tauhidi suma su yi kokari a fagen yin adalci.
Your Comment