Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro da ke ziyara a nan Iran inda yayin da yake ishara da irin shan kashin da Amurka take ci gaba da yi a kokarinta na tabbatar da iko da kuma siyasarsa a yankin Yammacin Asiya ya ce: Wasu suna tunanin cewa ba za a iya yin nasara a kan Amurka ba, alhali kuwa hakan babban kuskure ne.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Kura-kuran da Amurka take ci gaba da yi a wannan yankin tsawon shekaru 15 din da suka gabata, su ne suka sanya ta cikin tsaka mai wuyan da a halin yanzu take ciki a yankin.
Yayin da ya koma kan batun faduwar farashin mai kuwa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar an kirkiro wannan matsala ta kayar da farashin man fetur din ne da nufin yin matsin lamba ga kasashe masu arzikin man fetur da sauran 'yantattun kasashe yana mai cewa kasar Venezuela a matsayinta na shugabar kungiyar kasashe 'yan ba ruwanmu za ta iya taka gagarumar rawar wajen cimma manufofin wadannan kasashen.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Venezuelan Mr. Nicolas Maduro ya jinjina wa irin tsayin dakan gwamnati da al'ummar Iran wajen tinkarar matsin lambar Amurka yana mai cewa a halin yanzu Iran tana cikin kwanciyar hankali da tsaro sama da sauran kasashen da suke makwabtaka da ita.
A jiya ne dai shugaban kasar Venezuelan ya iso nan Iran don ganawa da manyan jami'an kasar.288