Rahotonni daga Amurka suna bayyana cewar tun a ranar Litinin da dare dubban jama’a suka kwarara a kan tituna a sassa daban daban na kasar tare da gudanar da kone-kone da kuma arangama da ‘yan sanda domin nuna fushinsu kan matakin da kwamitin alkalai mashawarta kan harkokin shari’a a garin Ferguson da ke jihar Missouri ya dauka na wanke dan sanda farar fata Darren Wilson daga zargin laifin aiwatar da kisan ganganci kan Michael Brown matashin bikin fata dan shekaru 18 a duniya.
Tun a ranar 9 ga watan Agustan wannan shekara ce wani jami’in ‘yan sandan garin Ferguson da ke jihar Missouri ta kasar Amurka Darren Wilson ya harbe Michael Brown har lahira, amma kwamitin alkalai mashawarta kan harkokin shari’a a garin ya zartar da hukuncin cewa laifin kisar bai kai wanda za a gurfanar da jami’in ‘yan sandan a gaban kotu domin fuskantar shari’a ba.
A halin yanzu haka dai kasar Amurka ta dauki zafi inda kungiyoyin kare hakkin bil-Adama, jama’ar kasa a sassa daban daban na Amurka suke ci gaba da gudanar da zanga-zanga da kone-kone tare da dauki ba dadi da ‘yan sanda domin nuna fushinsu kan yadda ake ci gaba da nuna bakar siyasar zalunci na bambancin launin fata a kasar ta Amurka. Abna