A jawabinsa a yayin bude zaman Majalisar Shawarar ta Musulunci a jiya Laraba: Dr Ali Larijani ya fayyace cewa yau fiye da shekaru uku ke nan gwamnatin Amurka da wasu kawayenta suna taimaka wa ayyukan ta’addanci a kasar Siriya. Sannan wasu daga cikin kasashen da suka shiga cikin sahun kawancen Amurka kan yaki da ta’addanci, suna daga cikin kasashe masu goyon bayan ayyukan ta’addanci a kasar ta Siriya, kuma mafi yawan ‘yan ta’addan kasa da kasa ta cikin kasashensu suka tsallaka zuwa cikin kasar Siriya.
Dr Larijani ya kara da cewa; Shin gwamnatin Amurka tana zaton wani zai gaskata da’awarta ta yaki da ta’addanci ne, alhali har yanzu tana kan bakanta na ci gaba da taimaka wa ayyukan ta’addanci, inda ko a cikin makon da ya gabata sai da ta sake gabatarwa Majalisar Dokokin kasar ta Amurka bukatar ci gaba da tallafawa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya. ABNA