Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahllul Bayt As – ABNA - ya habarta cewa: Birnin Karbala mai tsarki ya samu cikar maziyarta da dama don gudanar da raya daren Alhamis a hubbaren Abal-Fadl Abbas (amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Birnin na Karbala yana karbar dimbin maziyartan da ke zuwa ziyarar hubbaren Imam Husain da kuma dan uwansa Abal Fadl Abbas (amincin Allah ya tabbata a gare su) a cikin watan Muharramil Haram, domin nuna nuna biyayya ga Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su).
Atbatul Abbasiyya (a.s) ta shirya wani gagarumin shiri na maraba da masu ziyara a cikin watan Muharram, don samar musu da ingantattun hidimomi da biyan bukatunsu.








Your Comment