Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Ahmad al-Fatlawi, mai magana da yawun gwamnatin lardin Najaf Ashraf, a cikin hira da gidan talabijin na Rudaw, ya sanar da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen tsaro, ayyuka da tsari don gudanar da jana'izar Ayatullahil-Uzma Shahid Sayyid Ali Khamene'i, jagora shahidin juyin juya halin Musulunci, kuma lardin Najaf yana shirye don karbar bakuncin wannan taron tarihi.
Yana mai nuni ga gudanar da tarurruka na yau da kullun tsakanin jami'an lardin, hukumomin tsaro, cibiyoyin ayyuka, zamantakewa da kungiyoyin maukibobin Hussaini, ya ce: Tun lokacin da aka sanar da lokacin taron, an gudanar da tuntuba mai yawa, kuma kwanaki uku da suka gabata, an sanar da cikakken shirye-shiryen dukkan hukumomin da abin ya shafa.
Al-Fatlawi ya bayyana cewa za a gudanar da taron maraba da jana'izar a hukumce, da karfe 9 na dare ranar Talata a filin jirgin sama na kasa da kasa na Najaf Ashraf, tare da halartar manyan jami'an Iraki da kwamitoci daga kasashe daban-daban.
Ya kara da cewa: Za a fara jana'izar jama'a da karfe 6 na safe ranar Laraba, kuma ana sa ran fiye da miliyan ɗaya za su halarta.
Mai magana da yawun gwamnatin lardin Najaf ya kuma ba da rahoton fara shigowar kwamitocin hukuma da na jama'a zuwa wannan birni tun daga jiya, kuma ya ce: Tawagogi daga larduna daban-daban na Iraki da kuma wasu kasashe sun shigo Najaf don halartar wannan taron.
Ya bayyana cewa kwamitin tsaro na hadin gwiwa, ya tsara kuma ya kammala hanyar tafiyar da gawar jagora shahidin juyin juya hali daga filin jirgin sama na kasa da kasa na Najaf zuwa haramin Amiril-Mu'minin (A.S), sannan zuwa Karbala mai tsarki, sannan kuma zuwa Mashhad mai tsarki a Iran.
Al-Fatlawi a ƙarshe, yana mai nuni ga shigar dukkan bangarorin hukumomin tsaro na Iraki wajen aiwatar da tsarin tabbatar da tsaron taron, ya ce, baya ga sojojin da ke Najaf, an kuma aike da dakarun taimako daga Bagadaza da sauran larduna don aiwatar da tsarin tsaro, kuma ƙwarewar Najaf wajen gudanar da bukukuwa da ziyarori na miliyoyin mutane, ta samar da damar gudanar da wannan taro cikin tsari da aminci.
Dangane da sanarwar jami'an Iraki, za a kai gawar shahidin al'umma Ayatullah Khamene'i zuwa Najaf da yammacin ranar Talata, kuma za a gudanar da jana'izar a hukumce ta manyan jami'an kasashen Iran da Iraki. A kan haka, za a yi jana'izar gawar Imam Shahidi da karfe 6 na safe ranar Laraba tare da halartar miliyoyin 'yan Iraki daga Kufa zuwa Najaf, sannan bayan haka da karfe 4 n yamma agogon Iraki za a yi rakiyar jana'izar gawar sa a wasu yankuna na birnin Karbala mai tsarki, sannan a kabarin Sayyidush-Shuhada (A.S) da kabarin Sayyid Abul Fadlil-Abbas (A.S).
......
Your Comment