5 Yuli 2026 - 17:24
Source: ABNA24
Iraki: An Jibge Sojojin Hashdush-Sha'abi 30,000 Don Tabbatar Da Tsaron Jana'izar Shahidin Jagora A Najaf Da Karbala

Rundunar Hashdush-Sha'abi ta Iraki a yankin Furat ta Tsakiya, tare da hadin gwiwar kwamandancin ayyukan hadin gwiwa na sojojin Iraki, ta ajiye sojojinta 30,000 tun daga safiyar yau a garuruwan Najaf, Karbala da yankunan da ke kewaye, don tabbatar da tsaron jana'izar da bankwana da gawar shahidin jagora juyin juya halin Musulunci.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Rundunar Hashdush-Sha'abi ta Iraki a yankin Furat ta Tsakiya, tare da hadin gwiwar kwamandancin ayyukan hadin gwiwa na sojojin Iraki, ta ajiye sojojinta 30,000 tun daga safiyar yau a garuruwan Najaf, Karbala da yankunan da ke kewaye wadannan garuruwa, kuma har zuwa karshen jana'izar da bankwana da gawar shahidin al'umma, za su dauki alhakin tabbatar da tsaron taron da kare masu makoki.

A lokaci guda, a Najaf Ashraf, Maukibobin Iraki 100 da Maukibobin Iran 25 sun bayyana shirye-shiryensu don ba da ayyuka da karbar bakuncin masu makoki.  Haka kuma gwamnatin lardin Najaf ta ba da gine-gine 25 da ke da alaka da ma'aikatar ilimi ga masu gudanar da ayukan Iran, don amfani da su a matsayin wuraren kwana da hutawa ga kwamitocin da suka zo daga Iran.

A wannan fanni, larduna 10 na Iraki ciki har da Bagadaza, sun ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu don 'yan ƙasa su iya halartar jana'izar da bankwana da shahidin al'umma a Najaf da Karbala.

…………………..

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha