Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: A yayin zaman, Wakilin Yan'uwa Musulmi na Kazaure, Sheikh Magaji Mai Wada, ya gabatar da muhimmin jawabi ga mahalarta taron, inda ya yi bayani kan darussa da sakonnin da ke kunshe a juyin Karbala, tare da jaddada muhimmancin tsayawa tsayin daka kan gaskiya, adalci da gwagwarmayar kare addini kamar yadda Imam Husaini (AS) ya koyar.
Zaman ya gudana cikin yanayi na jimami da alhini kan abubuwan da suka faru ga Ahlul Baiti (AS), yayin da mahalarta taron ke sauraron jawabai da kuma tuna sadaukarwar shahidan Karbala.
Ana sa ran ci gaba da gudanar da sauran shirye-shiryen da aka tanada a zaman na yau, tare da addu'o'i da neman rahamar Allah ga shahidan Karbala da sauran shahidan Harkar Musulunci.
10/Muharram/1448
25/June/2026
Your Comment