Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: A cewar wasu majiyoyi na kusa da tawagar tattaunawar, tawagar Iran ta bar wurin tattaunawar ne don nuna adawa da barazanar Trump.
Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake mayar da martani ga barazanar Trump a shafinsa na sada zumunta, ya rubuta: Ba ma daukar barazanar Amurkawa da komai; muna shirye don mayar da martani.
Shugaban tawagar tattaunawar Iran ya rubuta: Ashe ba su tunanin cewa idan barazanarsu ta na da wani sakamako, da ba za su kai ga rashin ƙarfin da suke ciki yau ba? Ba mu la'akari da barazanar Amurkawa da komai.
Qalibaf ya jaddada cewa: Gara su kula da maganganunsu, sojojinmu suna shirye don mayar da martani ta wata hanya dabam. Ko me suka faɗa, mu kuma aiki za mu yi.
.......................
Your Comment