21 Yuni 2026 - 23:37
Source: ABNA24
Sheikh Qassem: Shirin Amurka Da Isra'ila A Kan Iran Da Fagen Gwagwarmaya Ya Sha Kaye

Babban Sakataren Hizbullah Lebanon, yayin da ya jaddada cewa shirin hadin gwiwar Amurka da Isra'ila don raunana Iran da kuma jigon gwagwarmaya ya sha kaye, ya sanar da cewa Iran, duk da matsin lamba mai yawa da hare-haren soji, ta kare hakokinta da ƙarfi, kuma fagen gwagwarmaya ma, ta hanyar tsayin daka a kan gwamnatin yahudawa, ya shiga sabon matakin ma'auni na yanki.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Babban Sakataren Hizbullah Lebanon a cikin jawabinsa na yau - Lahadi 21 ga Yuni, 2026 - yayin da ya jaddada cewa gwagwarmaya halastaccen kare kai ne ga 'yancin rayuwa da 'yanci wajen fuskantar mamaya da kasashen waje, ya na mai sanar da cewa Iran, duk da dubban hare-hare sama da ta dogara da jagoranci da juriyar al'ummarta, ta samu damar ficewa daga fagen yaƙi da ƙarfi fiye da da.

Sheikh Naim Qassem, Babban Sakataren Hizbullah, yayin da yake nuni da tushen tunani da imani na gwagwarmaya, ya bayyana cewa: Juriya da gwagwarmaya, kare kai ne na halal ga 'yancin rayuwa da 'yanci a wajen fuskantar mamaya, kakaba sharuɗɗa da y’an kasancin kasashen waje.

Ya kara da cewa: Wannan yunkuri mai tushe yana dogara ne akan koyarwar Imam Hassan da Imam Hussain (a.s) da kuma hanyar tarbiyyar Musulunci.

Babban Sakataren Hizbullah ya bayyana cewa: Tarbiyyar da tushenta soyayya ce da sanin zuciya, ba iya biyayya kawai ba. Wannan gamayyar zuciya da Ahlul-Bayt (a.s), yana haskaka hanyar tafiyar al'umma har zuwa lokacin fitowar Imam Mahdi (A.J) da jiran fitowarsa.

Iran Ta Kare Hakokinta Da Ƙarfin Izza

Sheikh Naim Qassem, yayin da ya bayyana cewa gwamnatin yahudawa, don raunana fagen gwagwarmaya, tare da goyon bayan Donald Trump, ta tayar da yaƙi a kan Iran, ya ce: Netanyahu da tunanin cewa bugun Iran a matsayin cibiyar gwagwarmaya zai haifar da rugujewar sauran sassan, ya yi kokarin lalata gwagwarmaya gaba daya a duniyar Musulunci.

Ya ci gaba da cewa: Duk da aiwatar da hare-hare sama da 25,000 na sama, Iran, ta dogara da jagoranci na musamman da juriyar al'ummarta, ta fice daga wannan fagen da ƙarfi fiye da da, kuma ta karɓi ragamar mulki.

Babban Sakataren Hizbullah Lebanon ya kuma bayyana cewa: A lokaci guda, gwagwarmaya a Lebanon ma, tare da sadaukar da shahidai masu daraja kamar Sayyid Hassan Nasrallah da sadaukarwar mujahidai, sun yi wa makiya mummunan rauni, kuma a ƙarshe, wannan babban shirin Amurka da Isra'ila ya sha kaye.

Gwagwarmaya Ba Za Ta Yarda Da Ma'anar Tsagaita Wuta Ta Yahudawa Ba

Ya kuma yi nuni da abubuwan da ke faruwa a Lebanon da yankin, ya jaddada cewa: Shirin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila don lalata Iran, Hizbullah da fagen gwagwarmaya a yankin ya sha kaye, ya zamo kuma an sami sabon mataki.

Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa: Makiya sun yi ƙoƙari ta hanyar ba da ma'anar tsagaita wuta ta gefe ɗaya a Lebanon, su hana Hizbullah harba makamai, kuma a lokaci guda, su kiyaye 'yancin Isra'ila na kai hari da ci gaba zuwa kowane wuri. Gwagwarmaya ta ɗauki wannan hanya a matsayin ci gaba da ta'addanci, kuma ba zai taɓa yarda da ita ba.

Ya yi ishara da cewa: Fagen gwagwarmaya a cikin watanni 15 na haƙuri, ya bayyana matsayinsa game da hanyoyin da aka ba da shawara a fili.

Babban Sakataren Hizbullah na Lebanon ya bayyana cewa: Tsagaita wuta dole ne Isra'ila ta fara, kuma idan gwamnatin yahudawa ta yarda kuma ta mutunta shi da gaske, to gwagwarmaya ma za ta bi hanyar zaman lafiya.

Jaddada Tsagaita Wuta Ta Gaske Da Fitar Da Mamaya Gaba Daya

Sheikh Naim Qassem, yayin da ya bayyana cewa gwagwarmaya tana ƙin wuce gona da iri na gwamnatin yahudawa, ya bayyana cewa: A cikin watanni 10 da suka gabata, gwagwarmaya ta tsaya tsayin daka a kan gwamnatin yahudawa mai ta'addanci da neman mamaya, wadda ke yunkurin shirin "Babbar Isra'ila" da mamaye yankin, kuma ba ta yarda da kowane irin bayar da cin hanci ba.

Ya kara da cewa: Ba za mu taɓa komawa yanayin da ake ciki kafin 2 ga Maris ba; yanayin da Isra'ila, tare da iƙirarin tsagaita wuta, amma ta ci gaba da kiyaye 'yancin ayyukan hare-haren ta.

Babban Sakataren Hizbullah na Lebanon ya ci gaba da cewa: A wurinmu, tsagaita wuta ta gaske tana nufin dakatar da hare-hare na ƙasa, sama da ruwa gaba daya, kawo ƙarshen mamaya, rashin ci gaban makiya, da fitar da sojojin yahudawa cikin sauri daga Lebanon ba tare da ko da wani sansani ba.

Ya yi ishara da cewa: A kan haka, an girke sojojin Lebanon a kudancin kogin Litani; amma game da batutuwa kamar kwance damarar gwagwarmaya, matsayinmu har yanzu yana kan murkushe ayyukan ta'addancin Isra'ila.

Goyon Bayan Iran Ga Fagen Gwagwarmaya

Sheikh Naim Qassem, yayin da ya jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga fagen gwagwarmaya, ya ce: A yau fagen gwagwarmaya yana samun babban goyon bayan jagoranci, al'umma da kuma dakarun juyin musulunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ya kara da cewa: Gwamnatin yahudawa a cikin watannin da suka gabata ba ta kawo komai ba face yaudara da harin diflomasiyya, kuma tana neman shiga cikin harkokin cikin gida da tafiyar da ƙasar Lebanon; yayin da Isra'ila ba ta sami wata nasara ba, bai kamata a bar ta ta yi irin wannan shiga ba.

Babban Sakataren Hizbullah na Lebanon ya bayyana cewa: Gwamnatin Lebanon, maimakon roƙon makiya, ta dogara da ƙarfinta da goyon bayan Iran, wadda ta ma rufe mashigar Hurmuz saboda Lebanon, ta yi aiki da kanta.

Ya kuma bayyana cewa: Hare-haren rashin tausayi na gwamnatin yahudawa suna ci gaba ne kawai da goyon bayan Amurka.

Sheikh Naim Qassem ya ci gaba da cewa: Washington, a ƙarƙashin sunan tattaunawa, tana neman cimma bukatunta na mulkin mallaka a Lebanon da dukan yankin, kuma idan Trump ya tilasta wa Netanyahu dakatar da yaƙi, gwamnatin yahudawa ba za ta iya ci gaba da waɗannan ta'addanci ba.

Ƙarfin Iran Ya Kai Amurka Teburin Tattaunawa

Babban Sakataren Hizbullah na Lebanon, yayin da yake nuni da abubuwan da ke faruwa a siyasance a yankin, ya ce: Amurka ta shiga tattaunawa da Iran kuma ta sake duba dangantakarta ta shekaru 47. Gaskiyar siyasar Lebanon tana nuna cewa babu wani yunkuri na cikin gida da zai iya rinjayar ɗayan.

Ya kara da cewa: Jin daɗi da inganta yanayin Lebanon ba za su samu ba sai a inuwar zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da rashin dogaro ga waje, domin bisa dogara da wannan haɗin kai da tsaya tsayin daka a kan makiya yahudawa ne za’a iya kwato ikon ƙasa.

Sheikh Naim Qassem ya ci gaba da yaba wa matsayin wasu shugabannin siyasar Lebanon, ya ce: A wannan hanya, matsayin tushe na shugabanni masu daraja kamar Mista Franjieh wajen fuskantar takunkumi da dakewa a kan ƙa'idodin ƙasa, sun cancanci yabo.

A ƙarshe ya jaddada cewa: Haɗin kai tsakanin matasan Lebanon, Hizbullah, ƙungiyar Amal da kuma dakarun tsaro, sun sa fagen gwagwarmaya ya zama wanda ba a iya kayar da shi. Ta hanyar dogara da matsayi madaidaici da kuma manne wa makarantar Ashura da kuma tarihin Imam Hussain (A.S), wannan ƙarfin zai dawwama.

..........................

Your Comment

You are replying to: .
captcha