Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin Isra'ila a cikin sabon rahotonsu game da asarar da suka yi a fagen Lebanon, sun tabbatar da cewa wasu daga cikin sojojinsu sun samu raunuka sakamakon harin jirgi mara matukin Hizbullah.
Bayan fashewar wani jirgi maras matuki da ya kai hari a kudancin Lebanon, gungun hafsoshi da sojoji 6 na sojojin Isra'ila sun samu raunuka mai tsanani.
Kafofin yada labara Isra'ila sun ba da rahoton cewa sojoji 10 na wannan rukuni sun samu raunuka a kudancin Lebanon.
Rahotonnin sun ce tun daga safiyar yau Laraba, sojoji 10 na sojojin Isra'ila sun samu raunuka a matakai daban-daban.
Dangane da wannan rahoton, da yammacin juya Alhamis kuma sojoji 7 sun samu raunuka a kudancin Lebanon.
Kungiyar Musulunci ta Lebanon ta sanar da cewa a jiya, ta kai hare-hare 24 a kan sojojin mamaya a cikin ƙasar Lebanon.
A cikin waɗannan hare-hare, an kai hari kan tankokin Merkava 7 da motocin bulldoza 2.
Haka kuma, an kai hare-hare 12 kan gungun sojoji da motocinsu.
Wani jirgin Hormuz 450 na Isra'ila a sararin yankin tsakiya na kudancin Lebanon, ma an kai masa hari da makami mai linzami na Hizbullah.
Sau 4 kuma Hizbullah ta kai hare-haren rokoki da jirage marasa matuka kan sabbin sansanonin da wuraren kafa manyan bindigogin sojojin Isra'ila.
Hizbullah bisa amfani da jirage marasa matuka masu fashewa, sun kai hari kan wurare da kan kafaffun manyan bindigogin harba rokoki na sojojin Isra'ila a garin Bint Jubeil a kudancin Lebanon.
Wasu gungun sojojin Isra'ila da suka kutsa zuwa garin Hadatha, ma an kai musu hari tare da dakatar da su ta hanyar amfani da manyan rokoki.
A kewayen garin Hadatha, Hizbullahi ta lalata wata motar bulaudoji da tankokin Merkava guda biyu na sojojin mamaya kuma wadanda ke cikinsu sun mutu.
Sashen leƙen asiri na Hizbullah, ta hanyar sa ido sosai kan motsin sojojin mamaya, sun buɗe hanya ga jirage marasa matuka masu kai hari. kisa na gwagwarmaya don su kai hari ga kwamandojin fagen daga daya bayan daya. Tun daga kwamandan bataliya ta 300 a Shomira, zuwa kwamandan bataliya ta 401 wanda har yanzu yana cikin suma bayan kai masa hari.
Hizbullah ta Lebanon ta sanar da cewa ta kai hari kan wata motar soja ta sojojin Isra'ila a garin Dabal, da gungun motocin makiya guda biyu a kusa da tashar jiragen ruwa na garin "al-Naqoura" da garin "Tir Harfa", bisa amfani da jirage marasa matuka.
Hizbullah ta Lebanon a cikin wani rahoto game da ayyukan yau da kullum na gwagwarmaya, ta sanar da cewa mayakan gwagwarmayar Musulunci a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, sun gudanar da ayyuka 16 daban-daban na soji a kan sansanonin, wurare, da wuraren taruwa da zaman sojojin Isra'ila a yankunan iyaka da arewacin Falasdinu da Isra'ila ta mamaye.
........................
Your Comment