A jawabinsa, ya bayyana watan Dhul-Hijja a matsayin wata mai falala, wanda kuma muhimman abubuwa da dama suka faru a cikinsa. Daga ciki akwai auren Imam Ali (A.S) da Sayyida Zahra (S.A), wanda ya ce aure ne “da ya koyar da mu yadda ake aure a Musulunci.” Yayin da ya ke bayani kan sadaukarwar Annabi Ibrahim (A.S) ta layya da ɗansa, Annabi Isma’il (A.S), wadda ta afku a wannan wata, ya ce ma’anar layya ita ce sadaukarwa, kamar yadda Annabi Ibrahim (A.S) ya koyar. Ya ce: “Layyarmu a yau ita ce ƙudurta sadaukar da duk abin da mutum ya mallaka ga addini.”
A ci gaban jawabin sa, ya yi bayani kan fifiko da darajar Ahlul Baiti (A.S), wanda ya ce su ne zaɓin Allah bisa hikimarsa, kuma Ya sanya binsu a matsayin hanyar tsira. Ya ce: “In Allah ya ajiye daraja, idan kana son ka tsira, kar ka yi musu. Idan ka yi hassada, to ka bi sunnar Iblis.” Ya kawo misalin yadda Yahudawa suka yi hassada ga Manzon Allah (S) saboda bai kasance daga cikinsu ba. Haka nan, Iblis ma ya yi hassada ga Annabi Adam (A.S), wanda hakan ya jawo halakarsa. A ƙarshe, ya jaddada cewa: “Son Ahlul Baiti aiki ne; za ka sallama ranka ne, ka bi.”
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
03/DhulHijja/1447
20/05/2026
Your Comment