19 Mayu 2026 - 11:39
Source: ABNA24
Ɗaliban Fudiyya Sun Yi Mauludin Imam Ali Ridha (as) A Garin Yelwa Mai Bene + Hotuna

A jiya Litinin 18/05/2026, ɗalibai Yara Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), na makarantar Fudiyya da ke garin Yalwa Mai Bene, ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna, sun gudanar da Mauludin Imam Ali Arridha (as)

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa:  Wanda ya kasance cikin gasar da suke gudanarwa a mabanbanta House da suke da shi, Taron ya kasance cikin tsari na musamman, cike da nishadi, da ado Mai kyau.

‎A yayin wannan mauludi, ɗaliban sun nuna bajinta da ƙwarewa ta hanyar gabatar da abubuwa masu matuƙar jan hankali da ilmantarwa.

An gudanar da taron cikin kyakkyawan yanayi wanda ya bayyana yadda ɗaliban suke da himma da ƙwazo wajen neman ilimi da kuma fahimtar yadda  gwagwarmayar tabbatar da addinin Musulunci ke ciki.

‎Wannan mauludi ya kasance wata hanya ta ƙara wa ɗaliban ƙwarin Gwiwa, haɗin kai da kuma bunƙasa fahimtarsu ta addini da karatu da sanin yadda ake son ɗan gwagwarmaya ya kasance cikin tarbiyya, da biyayya da jajircewa.

Daga: Salisu A Ɗahiru

19 - 5 -2026 / 2st Zulhijja 1447

Zaria Media Forum

Your Comment

You are replying to: .
captcha