Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Babbar manufar wannan sansani ita ce tallafawa jiragen yaƙi da kuma jibge sassan dakaru na musamman masu bincike da ceto, bayan fadowar jiragen ko kuma makalewar matuƙan Isra'ila a cikin ƙasar Iran, za su iya shiga cikin aiki nan take domin ceto su.
Wannan sansanin soji, wanda aka gina shi a kan busasshen tafkin yana da nisan kilomita 180 daga kudu maso yammacin Najaf, ya ƙunshi titin jirgin sama na wucin gadi mai tsawon kilomita 1.6 da katangar ƙasa. Saboda yanayin wurinsa na ƙasa, yana da matuƙar wuya a iya gano shi. Duk da haka, kasancewar aikin wannan sansani takaitacce ne sosai; domin kwanaki 20 kacal bayan fara yaƙin, ruwan sama mai ƙarfi ya sa busasshen tafkin ya zama laka, kuma titin jirgin ya zama ba a iya amfani da shi, wanda hakan ya sa wannan shirin dabara ya ci tura.
Hakikanin Labarin Sansanin Sirri Na Isra'ila A Iraki
Kwanan nan jaridar Wall Street Journal a cikin rahoton bincikenta ta tona asirin wanzuwar wani sansanin soji na ɓoye na Isra'ila a cikin ƙasar Iraki. Bisa ga wannan rahoto, Isra'ila ta gina wannan sansani ne musamman don tallafawa dabaru ga ayyukan yaƙi da jiragen sama a kan Iran.
Abin da ya kamata a yi la'akari shi ne, titin jirgin sama na ƙasa a kan busasshiyar tafkin, ana iya gina shi cikin sauƙi amma yana da wuyar ganowa. Amma Iraki ta ƙaryata wanzuwar sansanin soji na Isra'ila a cikin ƙasarta
Wannan shi ake kira bay a da kura domin kuwa Sakamakon iƙirarin da wasu kafafen yada labarai na waje suka yi game da wanzuwar sansanin soji na gwamnatin sahyoniya a cikin ƙasar Iraki, Birgediya Janar "Sa'ad Ma'an", shugaban ma'aikatar watsa labarai ta tsaro na kwamandan haɗin gwiwa na Iraki, a ranar Lahadi ya fitar da sanarwa a hukumance inda ya ƙaryata waɗannan rahotanni.
Your Comment