5 Afirilu 2026 - 00:02
Source: ABNA24
Hizbullah Ta Kai Hari Kan Ma'aikatar Yaƙin Isra'ila + Bidiyo 

Hizbullah: ta kai hari kan cibiyar yaƙin Isra'ila da wani sansanin leƙen asirin Isra'ila 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hizbullah ta kai hari wa taron sojojin sahyoniyawa da motocinsu masu sulke na wannan gwamnati a wurin sojin Al-Malkiya da makamai masu linzami. 

Hizbullah ta sanar da gudanar da wasu ayyuka guda biyu a kan sahyoniyawa inda ta kai hari kan taron sojojin Sahayoniya a kan tudun Fariz a garin Ainata da rokoki da dama. A wani aikin kuma, Hizbullah ta kuma kai hari kan mayakan sahyoniyawava yankin Al-Sadr da rokoki da makamai masu linzami. Sannan Hizbullah sun yi arangama da gungun sojojin Isra'ila a kusa da Tahrir Triangle tare da haifarwa da sojojin abokan gaba asarar rayuka da raunuka. 

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kuma bayar da rahoton asarar rayuka a tsakanin sojojin Sahayoniyawa a arangamar, inda ta ce a lokaci guda mayakan gwagwarmaya sun kai hari kan dakarun kawo ɗauki na Isra'ila da makamai masu linzami da manyan bindigogi, bayan haka jirgin sama mai saukar ungulu na Isra'ila ya sauka domin kwashe wadanda suka mutu da jikkata. Hizbullah tana amfani da dabarar yaƙi na Rasha ta hanyar amfani da jiragen yaƙi marasa matuka nau'in FPV drones tare da tsarin fiber optic da warhead. Wanda ke iya ajiye jirage marasa matuka akan hanya ko a cikin kwanton bauna da ake sarrafa su kyamara daga nesa. Filin daga na Hizbullah a fagen yaƙi da kuma a kafafen yada labarai ya fi sauran kasashen tsakiya fadi. Kwarewar yakin kwanaki 66 ya gyara kurakuran da suka gabata da kuma arangama kai tsaye da ta ƙasa da abokan gaba. Abubuwan da kafafen yada labarai suka wallafa a watan farko na rikicin ya ninka na yakin kwanaki 66, kuma kungiyar Hizbullah ce kan gaba a wannan arangama.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha