Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Jami’an Tsaron sarrain samaniyar Iran a Tehran suna ci gaba da fuskantar da aranagama da ba da kariya ga hare-hare masu ta’addancin Amurka da Sahyoniya tun bayan fara kai hare-haren da Amurka ta yi wa Iran.
A safiyar ranar Asabar, Amurka da Isra'ila sun kaddamar da hare-hare da dama a yankunan Tehran, biranen Isfahan, Qom da Kermanshah. Mintuna kadan bayan wannan tashin hankali, sojojin Iran sun fara kai hare-haren makamai masu linzami kan Isra'ila, inda suka kai hari kan Haifa, Tel Aviv, da wasu sansanonin sojin Amurka da ke yankin. Kwamandan hedikwatar "Khatam al-Anbiya" Manjo Janar Ali Abdullahi, ya ce masu ta’addancin su jira wani gagarumin martani mai tsauri da tsanani daga dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda suka gani somin tabi ne.
Ra'ayinka