28 Faburairu 2026 - 21:36
Source: ABNA24
Bidiyoyin Hare-Haren Da Sojojin Iran Suka Kai Kan Wurare A Isra'ila Da Amurka A Yankin

Baya ga wurare masu yawa a yankunan da aka mamaye, sansanonin Amurka a Saudi Arabia, Jordan, Qatar, Kuwait, Iraki da sauran yankuna sun halaka ta hanyar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka na Iran.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Tun da tsakar rana a yau, biyo bayan hare-haren matsorata na gwamnatin Sahayoniya da Amurka kan kasar Iran, dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kai hari kan wurare da dama a yankunan da aka mamaye a wasu hare-haren makamai masu linzami daga sassa daban-daban na kasar. Bisa ga bayanan filin daga da rahotannin da aka samu daga sassa daban-daban na kasar, ciki har da Qom, Urmia, Ardabil, da sassa da dama na Iran ta tsakiya, makamai masu linzami na Iran sun tashi zuwa muhimman wuraren sahyoniya tare da kai hari kan muhimman cibiyoyin gwamnatin da suka hada da ma'aikatar yaki ta Isra'ila. Rahotanni daga kafafen yada labarai na Isra'ila sun ce, an harba makamai masu linzami 220 daga Iran zuwa kasar Falasdinu da ta mamaye daga safiyar yau Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026.

Tashar 15 ta gwamnatin sahyoniyawan ta kuma sanar da cewa: Iran na kai hari kan Tel Aviv da makamai masu linzami da dama. A sa'i daya kuma, majiyoyin Falasdinu sun ba da rahoton fashewar wasu abubuwa masu yawa a wani sansanin Amurka na Isra'ila kusa da birnin Al-Ad., Yedioth Ahronoth ta sanar da faruwar manya manyan sautuka a wani gini a cibiyar "Isra'ila" in  da Iran ta kai  hari kai tsaye da wani makami mai linzami.

A cikin rahoton da ta fitar kan hari na biyu na makami mai linzami na Iran, shafin yanar gizon Vala Zionist ya sanar da yammacin yau: "Muna ganin wani harin makami mai linzami a yankin "Great Tel Aviv" a tsakiyar Isra'ila. A lokaci guda tare da hari a cikin zurfin yankunan da aka mamaye, Har ila yau, sansanonin Amurka da ke yankin sun cika da harin makami mai linzami da jiragen sama da sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka kai hari, yaduwar guguwar fashewar makami mai linzami da hare-haren jiragen sama na Iran ya haifar a Dubai ya samu saurin bayyanuwa a kafafen yada labarai na kasa da kasa.

Har ila yau, kai harin kan sansanin Amurka da ke Bahrain na Daya daga cikin labaran da kafafen yada labarai suka yada labaransa, sansanonin Amurka da ke kasashen Saudiyya, Jordan, Qatar, Kuwait, Iraki da sauran yankuna a yankin su ma sun samu nasu kason na hari da makamai masu linzami na Iran da hare-haren jiragen sama. A daidai lokacin da Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin Amurka da ke yankin, majiyoyi a cikin rundunar sojin kasar sun sanar da cewa an kashe sojojin Amurka 200 tare da raunata wasu a hare-haren Iran da yammacin ranar Asabar.

Dangane da harin da Iran ta kai kan wuraren Amurka, Sakataren harkokin wajen Iran ya ce: "Harin da muke kai wa sansanonin Amurka a yankin, mataki ne na tsaron kariyar kai, ba za mu iya zama muna kallo ba." Har ila yau, mai magana da yawun hedkwatar Khatam Al-anbia ya sanar da cewa: aikin hare-hare da sojojin mu suke gabatarwa su yi za su ci gaba cikin karfi da zurfi.

A yammacin ranar Asabar, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami'in Turai yana cewa jiragen ruwa na samun sako daga jami'an tsaron juyin juya hali ta hanyar n’urar ruwa mai yawa, yana mai cewa babu wani jirgin ruwa da zai tsallaka mashigin Hormuz. Hare-haren da Iran ta kai kan Amurka da Sahayoniyawan makiya sun sa jami'an Amurka suka tsaya tsayin daka wajen fuskantar matakin Trump da Netanyahu tare d ayin tir da wannan yunkuri. Jami'an Amurka da manazarta, da kuma wasu jami'an Turai, sun kira harin Amurka da Isra'ila ga Iran da amari ne da ba za a amince da su ba, suna mai cewa cimma burin da ake so ya gaza tun ba a je ko ina ba, kuma sun ce: "Ba za mu iya jure wa wani dogon yaki ba!"

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha