1 Maris 2026 - 20:11
Source: ABNA24
Iran Ta Kakkaɓo Jiragen Yaƙin Amurka 22 Zuwa Yanzu

Dakarun Iran sun harbo jiragen sama marasa matuka goma bisa sanarwar mai lamba 5 na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a cikin 'yan sa'o'i da suka gabata, 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Dakarun Iran Sun kai hari kan wasu manyan jiragen sama marasa matuka 10 tare da harbo su a sassa daban-daban na kasar. 

Rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kara da cewa a cikin wannan sanarwar cewa wadannan jirage marasa matuka na cikin nau'in Hurmus ne kuma an harbe su tare da kabo su ta hanyar hadadden cibiyar sadarwa ta sansanin tsaron saman kasar da ke yankuna daban-daban na Tehran, Khuzestan, Isfahan, yammaci da arewa maso yammacin kasar da Fordow. Idan aka yi la’akari da yadda jiragen marasa matuka da aka Kakkaɓo jjiya, adadin jiragen da aka Kakkaɓo ya kai 22 tun farkon yakin.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha