18 Faburairu 2026 - 21:22
Source: ABNA24
An Ga Jinjirin Watan Ramadan A Iran + Bidoyo Da Hotuna

Da isowar watan mai albarka na Ramadan, an ga jinjirin wannan wata mai albarka a sararin samaniyar Ira a wurare da dama daga ciki akwai haramin Sayyidah Fatima Ma’asumah (A.S.) da  masallacin Jamkaran da wurare a lardunan Tehran, Qom, Isfahan da sauran yankunan ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Bisa sanarwar hedikwatar ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci gobe, Alhamis, 30 Bahman 1404 anda yayi daidai da 19 ga Fabraiun 2026 zai zama ranar farko ta watan Ramadan a Iran.

A cewar rahoton wakilin ABNA daga ayyukan ƙungiyoyin masu ganin wata, an ga jinjirin watan Ramadan mai tsarki a sararin samaniyar lardunan Tehran, Qom, Isfahan da sauran yankunan ƙasar ta amfani da kayan aikin da ake buƙata da kuma da gani ido kai tsaye, kuma gobe, Alhamis, za ta zama rana ta farko ta watan Ramadan mai albarka watan da Allah ya ke karbar bakunci bayinsa a cikinsa da yi masu karamci.

A nasa bangaren ma Ayatullah Sistani ya ayyana gobe a matsayin ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma

Ofishin Ayatollah Sistani da ke Najaf Ashraf ya kuma sanar da cewa, bisa la'akari da ganin jinjirin wata, yau (Laraba) ita ce ranar karshe ta watan Sha'aban kuma gobe (Alhamis) za ta zama farkon watan Ramadan mai alfarma 1447 AH.

Ƙasashen Musulunci da dama, ciki har da Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Diwan Sunni na Iraki, Siriya, Lebanon, da Falasdinu, sun ayyana ranar Laraba a matsayin ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma.

Hoto: Hamid Abedi

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha