Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar sojin Amurka ta sanar da ƙaddamar da wani sabon aiki a Siriya da nufin dauke fursunonin ISIS daga arewa maso gabashin ƙasar zuwa Iraki a ranar 21 ga Janairu, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da tsare fursunonin ISIS a wurare masu tsaro.
Rundunar ta bayyana cewa sojojin Amurka sun fara jigilar mayakan ISIS 150 da ake tsare da su a wani wuri da ke al-Hasakah, Siriya, zuwa wani yanki mai aminci a cikin yankin Iraki.
Ya nuna cewa shirin na iya ci gaba a nan gaba har sai dauke fursunoni har zuwa 7,000 daga ɓangarorin ƙungiyar a Siriya zuwa wurare da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin Iraki.
Kwamandan rundunar sojin Amurka ta tsakiya, Admiral Brad Cooper, ya ce "Amurka tana yin aiki kafada da kafada da abokan huldar yankin, musamman gwamnatin Iraki," yana mai nuna godiyarsa ga rawar da suka taka wajen "tabbatar da kawar da ISIS har abada".
Kober ya yi imanin cewa "sauƙaƙa jigilar fursunonin ISIS cikin tsari da aminci muhimmin umarni ne na hana duk wani keta doka da ka iya zama barazana kai tsaye ga Amurka da tsaron yankin".
Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa "mika gungun ‘yan ta’addan ga hukumomin Iraki da Amurkawa suka yi an gudanar da shi ne a hukumce, kuma ya kunshi wasu ‘yan kasashen Turai, Asiya, da Larabawa".
Sun kara da cewa "za a rarraba fursunonin ISIS a tsakanin Gidan Yarin Susa da ke Sulaymaniyah, Gidan Yarin Al-Hout da ke Nasiriyah, da Gidan Yarin Cropper kusa da Filin Jirgin Sama na Baghdad".
An ambaci cewa "hukumomin Iraki sun ware jagorori masu hadari na shugabannin ISIS daga wasu membobi, da wasu mutanen da ba su da hatsari".
Gwamnatin Iraki ta tabbatar da cewa yunkurin mayar da 'yan ta'addan ISIS daga yankin Siriya zuwa Iraki mataki ne na kariya da nufin kare tsaron kasar Iraki. Ta bayyana cewa ba a yanke wannan qudir ba bisa ka'ida ba sai dai an yi shi ne bisa nazari da tantancewa sosai, kuma an riga an fara shari'ar wadannan mutane.
........
Your Comment