22 Janairu 2026 - 22:46
Source: ABNA24
IRGC: An Kama Wasu Jagororin Masu Tarzoma 90 A Zanjan Da Kish

IRGC Cibiyar leken asirin IRGC Reshen Zanja: An kama shugabanni 90 masu tayar da tarzoma ayyukan ta'addanci a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wadanda suka keta harkokin tsaron jama'a, kona motoci da lalata dukiyoyin jama'a.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An gano tare da kama wadannan miyagun mutane. Har ila yau, daya daga cikin ginshikan masu neman mulki da ke cikin kasar, da ke ƙoƙarin samar da hanyar sadarwa da kuma ayyukan da ba su dace ba ya samu gabansa shi ma. 

Har ila yau an gano da kama shugabannin da manyan yan ta'addan da suka haifar da tarzoma a Kish kamar yadda cibiyar leken asiri ta Hormozgan IRGC tabbatar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha