21 Janairu 2026 - 21:07
Source: ABNA24
Trump: Greenland Tamu Ce, 'Yan Denmark Basu San Mutunci Ba 

Trump: Mun mayar wa Denmark Greenland ne bayan Yaƙin Duniya na Biyu. Kai amma mun zama wawaye a lokacin; amma duk da hakan mun yi. Yanzu ku duba yadda suke ['yan Denmark] marasa godiya!

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Trump yace Wannan babban tsibiri, wanda ba shi da tsaro a zahiri wani ɓangare ne na Arewacin Amurka, a kan iyakar arewacin Yammacin Duniya wacce ta ke a yankinmu!

Ina neman tattaunawa nan take don sake tattauna batun mallakar Greenland na Amurka. Kamar yadda muka mallaki yankuna da yawa a tsawon tarihi.

Abin da kawai muke so shine cikakken mallakar Greenland. Domin don kare wani yanki, dole ne ku mallake shi; ba za ku iya kare shi ta hanyar haya ba.

Trump kuma ya fuskantar da zancesa ga Firayim Ministan Kanada yana mai cewa: ya kamata ya tuna da wannan a lokaci na gaba da yake son yin magana game da Amurka.

Trump Ga Netanyahu: Iron Dome Na Amurka Ne, Ba Isra'ila Ba 

Shugaban Amurka: Amurka ba ta cimma komai ba a dangantakarta da NATO kuma ta biya kuɗin tsaron NATO duk waɗannan shekarun; amma yanzu buƙatarta kawai ita ce ta mamaye Greenland!

Muna da niyyar gina babban katafaren tsaro ne a Amurka.

Sannan Trump ya yi wa Firayim Ministan gwamnatin Benjamin Netanyahu gargadi cikin kakkausar murya mai raini: "Bibi! Kada Ka Ƙarasa Wannan Katafariyar Hasumayar Da Sunanka! Mu Ne Muka Gina Ta! Fasahar Amurka Ce

Trump: Greenland Tamu Ce, 'Yan Denmark Basu San Mutunci Ba 

Your Comment

You are replying to: .
captcha