21 Janairu 2026 - 19:39
Source: ABNA24
Iran: An Kama Tare Da Kashe 'Yan Ta'adda 12 Na Ƙungiyar Ansarush-Shaytan

Ma'aikatar Leken Asirin Iran : An kama mambobi 11 na wannan ƙungiyar ta'addanci-Takfiri a cikin ayyukan haɗin gwiwa guda 3 da Hedikwatar IRGC Quds. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Babbar Cibiyar Leken Asirin Lardin Sistan da Baluchestan da haɗin gwiwar yan sandan Furaja sun samu nasarar kashe ɗaya daga cikin shugabannin wannan ƙungiyar ta'addanci ta Takfiri, mai suna Sharur Gulmohammad Shahouzhi, da kuma kama sauran mambobinta 11 a wani fafatawa da jami'an tsaro.

Waɗannan 'yan ta'adda sun yi niyyar gudanar da ayyukan ta'addanci a Lardin Sistan Baluchestan kuma suna ɓoye a wajen Zahedan.

A maɓoyar waɗannan 'yan ta'adda, an gano makamin RPG, harsasai 24 na RPG, bindigogin Kalashnikov guda 2 da harsasai da bindigogin bel guda 6, da kuma adadin harsasai da kayan aiki da suka shafi ƙera bama-bamai.

Your Comment

You are replying to: .
captcha