Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ali Bahraini, yana mai Allawadai da hare-haren da Amurka da gwamnatin Isra'ila suka kai wa cibiyoyin nukiliya na Iran kwanan nan, ya bayyana waɗannan ayyukan a matsayin keta Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, dokokin ƙasa da ƙasa, da kuma babban koma-baya ga Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Makamai ta Nukiliya (NPT).
Da yake taya Mongolia murna kan karbar shugabancin taron kan kwance damarar makamai, Bahraini ya jaddada cikakken goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga kokarin farfado da rawar da wannan cibiyar ke takawa a tattaunawar, yana mai cewa: "Taron kan kwance damarar makamai, a matsayinta na cibiyar tattaunawa ta bangarori daban-daban a fannin kwance damarar makamai, dole ne ta ci gaba da yin shawarwari tare da gujewa zama cibiyar da ke da alkiblar tattaunawa kawai".
Wakilin Iran ya jaddada cewa: "Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga duk wani aiki na zalunci a cikin tsarin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, kuma wadatar da uranium don dalilai na zaman lafiya hakki ne da ba za a iya musantawa ba ga Iran a matsayinta na memba a NPT, wanda ba za ta taba rufe ido akan sa ba".
A lokaci guda, ya jaddada cewa Iran a shirye take ta yi tattaunawa ta gaskiya, ba tare da sharaɗi ba kuma bisa ga girmama juna.
Your Comment