21 Disamba 2025 - 11:30
Source: ABNA24
Al’ummar Morocco Sun Yi Zanga-Zangar Nuna Goyon Falasdinu

Dubban 'yan Morocco sun yi zanga-zangar a daren Asabar don nuna goyon baya ga mutanen Gaza da ake zalunta, da kuma kin amincewa da daidaita dangantaka da gwamnatin Isra’ila.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An gudanar da zanga-zangar ne da taken "Mutanen Morocco suna tare da gwagwarmaya da kuma kin daidaita dangantaka... Suna masu kare kasarsu da kuma goyon bayan Falasdinu". Zanga-zangar ta zo daidai da cika shekaru biyar da sanya hannu kan yarjejeniyar daidaita dangantaka tsakanin Morocco da gwamnatin Isra'ila a watan Disamba na 2020.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki a manyan titunan Tangier, suna rera taken goyon bayan fararen hula a yankin Gaza da kuma dora alhakin gwamnatin Isra'ila kan manufofinta na yunwa ga mutanen Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha