29 Satumba 2025 - 19:01
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kai Hari Kudancin Labanon Shahidai 2

Kamfanin dillancin labaran Quds: A Sabon harin da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon mutane 2 ne sukai shahada tare da jikkata mutam ɗaya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Majiyoyin labarai sun ba da rahoton wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan garin Nabatiyeh al-Fouqa da ke kudancin kasar Lebanon.

Sakamakon wannan harin mutane biyu sun yi shahada tare da jikkata mutum kamar yadda ita ma Ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon ta sanar a yau litinin cewa mutane biyu sun yi shahada sannan daya ya jikkata a harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a kudancin kasar.

Sa'o'i da suka gabata, gwamnatin Isra'ila ta kai hari kan "Sahmar", "Nabatieh al-Fouqa" da "Aytroun".

Your Comment

You are replying to: .
captcha