Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labaran Falasdinu sun bayar da rahoton shahadar akalla wasu 'yan kasar 73 su kai shahada sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a yankuna daban-daban na zirin Gaza da kuma harba makamai masu linzami a gidajen Falasdinawa a Ramallah.
Sojojin Isra'ila sun shahadantar da kalla Palasdinawa 73 a yankuna daban-daban na zirin Gaza a cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Jiragen yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila daga gabar tekun zirin Gaza sun kai hari kan birnin Khan Yunis da ke kudancin yankin.
Your Comment