Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: UNIFIL ta sanar a cikin wata sanarwa cewa: Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kudancin Lebanon ya sabawa kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 1701 da kuma yin barazana ga zaman lafiyar da ake samu.
Tun bayan kafa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin kasar da kasar Labanon, sojojin Isra'ila sun sha keta alfarmarta, suna kai hare-haren soji kan yankin na Lebanon tare da shahadantarwa da raunata wasu 'yan kasar. A halin da ake ciki, kwamitin da ke sa ido kan aiwatar da shirin tsagaita wutar bai dauki wani mataki na zahiri ba na dakatar da wadannan hare-hare.
Wannan kira dai ya biyo bayan jerin hare-haren ɗauki ɗaiɗai da Jirgin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi akan dakarun Hizbullah wanda na bayan na a yau jiragen sun kai hari kan wata mota a Tibnin da ke kudancin kasar Lebanon kuma hukuma tayi shiru kwamitin zartar da yarjejeniyar shima ya amsa tabuka komai.
Your Comment