Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce: Isra’ila ta kai harin bam a benayen sama na asibitin sau uku a jere, tsakanin 'yan mintuna kadan.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Falasdinu ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai wa asibitin yara na Al-Rantisi da yammacin jiya Talata. Tare da jaddada cewa laifin ya sake tabbatar da tsare-tsaren mamaya na lalata da gurgunta tsarin kiwon lafiya gaba daya a zirin Gaza.
Tayi ishara da cewa Asibitin Al-Rantisi shi ne asibiti na musamman a zirin Gaza, wanda ke ba da ilimin oncology, dialysis, da sauran fannoni kamar cututtukan numfashi da na narkewa.
Sanarwar ta ce, asibitin na dauke da majinyata 80 da ke karbar kulawa ta fannoni daban-daban, baya ga sassan kula da kananan yara hudu da na kananan yara jarirai takwas.
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta tabbatar da cewa, sakamakon tashin bam din, majinyata 40 sun bar asibitin domin neman mafaka da kuma lafiyar ‘ya’yansu. Ragowar majinyata 40, tare da abokan aikinsu, rukunin kula da marasa lafiya 12, da ma’aikatan asibiti 30 ne su ka saura.
Ma'aikatar lafiya ta sake sabunta kira ga dukkan bangarorin duniya da abin ya shafa da su ba da kariya ga cibiyoyin lafiya, ma'aikatan lafiya, da marasa lafiya a zirin Gaza.
Your Comment