Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: an gano gawarwakin kananan yara Palasdinawa a cikin asibitin Nasser da ke Khan Yunis a zirin Gaza. 'Yan tayi hudu da jarirai uku da ba su kai ba sun mutu a wurin. Rahotanni sun ce an danganta mutuwar jariran ne da rashin abinci mai gina jiki ga mata masu juna biyu, tsoro da kaura daga yaki, da yawan katsewar wutar lantarki, da kuma rashin magunguna da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi.






Your Comment