Hotunan Tauraron Dan Adam Da Ke Nuna Irin Barna Da Isra’ila Ta Yi A Gaza

Abun Ke Faruwa Ga Falasdinawa Cikakken Kisan Kare Dangine Da Aka Iya Yiwa Wata Al’umma
15 Satumba 2025 - 14:51
Source: ABNA24
Hotunan Tauraron Dan Adam Da Ke Nuna Irin Barna Da Isra’ila Ta Yi A Gaza

Hotunan tauraron dan adam da aka dauka a watan Satumba na Gaza sun nuna munin barnar da aka yi a birnin Gaza saboda mummnan kai hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kaiwa.

A cewar hukumar tsaron farar hula ta Falasdinu, akalla gine-ginen benaye 50 ne aka lalata a cikin 'yan makonnin nan, yayin da unguwanni irin su Al-Zaytoun da Al-Sabra Isra’ila ta lalata gidaje da gine-gine sama da 1,500 tun daga ranar 1 ga watan Agusta.  Dukka da cewa dubban iyalai ne suke yin hijira daga cibiyar Gaza da kudancinta amma dayawa daga cikinsu da basu samu wurin mafaka ba dole suka dawo gidajensu amma hanyar Salahadden da ta hada da hanyar Arrashed ba hanyoyi masu lafiya da aminci ba balle su biyo ta wajen. Mayakan sa-kai na Isra'ila sun jibge a mashigar Salah Din, ita hanyar Al-Rashid tana cike da tantinan 'yan gudun hijira kuma ana kai musu hari. Hatta yankin Al-Mawasi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta ayyana a matsayin wani yanki na jin kai mai aminci, an sha kai hare-hare, lamarin da ya sa al'ummar Gaza ba su da wata mafaka.

Hotunan Tauraron Dan Adam Da Ke Nuna Irin Barna Da Isra’ila Ta Yi A Gaza

Likitocin kasa da kasa sun tabbatar da cewe  Gaza tana fuskantar cikakken kisan gillar na gabaki dayan al'ummarta

Kungiyar Likitocin kasa da kasa ta bayyana abubuwan da ke faruwa a birnin Gaza a matsayin wani cikakken kisan gillar da aka iya yi wa wata al'umma tare da jaddada cewa Falasdinawa miliyan daya a birnin Gaza, wadanda suka kasa ficewa, suna rayuwa cikin fargaba da tsoro.

Kungiyar Likitocin kasa da kasa ta bayyana cewa sama da mutane miliyan daya a birnin Gaza na rayuwa cikin fargaba da tsoro bayan da gwamnatin Isra'ila ta ba da umarnin ficewa daga birnin.

Kubuta yana da matukar wahala kuma ba zai yiwu ba ga tsofaffi da masu fama da rashin lafiya, mata masu juna biyu da wadanda suka jikkata, kuma wadanda suka saura a Gaza suma kamar an yanke musu hukuncin kisa ne.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce wadanda ke kokarin tserewa suna fuskantar munanan hare-haren rokoki kuma ba su da tsaro, baya ga ba su da kayan da za su zauna a cibiyar Gaza da kudancin Gaza.

Abubuwan da ke faruwa a Gaza ba bala'in na rashin jinkai kawai, har ma da cikakken kisan kare dangi na al'umma gaba daya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha