Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bait As -Abna- ya habarta cewa: jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kaddamar da wani samame a birnin Damascus a ranar yau Larabar, inda suka nufaci ginin babban hafsan sojin kasar, da ma'aikatar tsaro da kuma kusa da fadar shugaban kasa.
A halin da ake ciki kuma ministan tsaron Isra'ila Yisrael Katz ya sanar da cewa an kawo karshen sakonnin gargadi ga Damascus tare da yin barazanar kai hare-hare masu zafi. Hakan ya biyo bayan sake barkewar rikici a Sweida da ke kudancin kasar.
Your Comment