Sojojin Ruwan Iran Sun Gabatar Da Atisayen Makamai Masu Linzami Na "Karfi Madawwami 1404" + Hotuna

An Yi Nasarar Kammala Atisayen Makami Mai Linzami Na "Ethgdar Paydar 1404" Na Sojojin Ruwan Iran
22 Agusta 2025 - 14:34
Source: ABNA24
Sojojin Ruwan Iran Sun Gabatar Da Atisayen Makamai Masu Linzami Na "Karfi Madawwami 1404" + Hotuna

An gudanar da atisayen ne a arewacin tekun Indiya da kuma tekun Oman ta hanyar harba makamai masu linzami iri-iri na gajeru zuwa dogon zango, "Nasiir da Ghadir" da makami mai linzami mai suna "Qader" da tafiya mai nisan kilomita 400

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: atisayen makami mai linzami na "Ethgdar Paydar 1404" da sojojin ruwan kasar Iran suka fara tun jiya Alhamis ya ci nasara tare da kawo karshe da cimma burin da aka sa gaba.

A cewar wannnan rahoto a ranar Alhamis din jiya ta bakin wakilin siyasa sashen hulda da jama'a na rundunar sojin kasar, atisayen makami mai linzami mai suna "Ethgdar Paydar 1404" da sojojin ruwa na kasar Iran suka yi ya kawo karshe tare da cimma burin da aka sa gaba.

An gudanar da atisayen ne a arewacin tekun Indiya da kuma tekun Oman ta hanyar harba makamai masu linzami iri-iri na gajeru zuwa dogon zango, "Nasiir da Ghadir" da makami mai linzami mai suna "Qader" da ke anfani da shi wajen tarwatsa jirgin ruwa da jirgin tarwatsa abubuwa mai suna "Bavar 5". A yayin atisayen, nau’oi daban-daban na jiragen kan ruwa da na karkashin ruwa, jirage masu masu tashi sama, jirage da makami mai linzami da kae harba su daga bakin teku zuwa teku, bangarorin makami mai linzami da ke kan teku, da makaman da ake anfani da su a daji sun yi nasarar aiwatar da hare-haren da aka kayyade.

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da wannan atisayen ya yi shi ne lalata wani wuri da aka zayyana a teku da makami mai linzami na "Nasir da Ghadir", da makami mai linzami na "Qader" da ke gabar teku da kuma makamin yaƙi da jiragen ruwa, da kuma jirgin "Bavar 5" mara matuƙi.

Babban matakan atisayen makami mai linzami na "Karfi Madawwami 1404" na sojojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran an gudanar da shi ne tare da nasarar aiwatar da aikin lalata wani wani wuri da makami mai linzami da jirgin "Bavar 5" da aka kayyade a arewacin tekun Indiya da kuma tekun Oman. A cikin wannan aiki, jirgin mara matuki na "Bavar 5" ya samu nasarar lalata inda aka zayyana bayan ya yi tafiya mai nisan kilomita 400.

Your Comment

You are replying to: .
captcha