ABNA24 : Kafin ganawar jami’an gwamnatin guda biyu a jiya Lahadi dai, a ranar jumma’ar da ta gabata ce ma’aikatar kudin Amurka ta sanya sunan Falih Al-Fayyad cikin jirin mutanen wadanda ta sanyawa takunkuman tattalin arziki, saboda a binda ta kira wai take hakkin bil’adama.
A shekarara da ta gabata ce gwamnatin kasar Amurkan ta kashe mataimakin Falih Fayyad, wato Abu Mahdi Al-Muhandis tare da bakon gwamnatin kasar Iraki Shaheed Qasim Sulaimani a tashar sauka da tashin jiragen sama na Bagdaza.
342/