ABNA24 : Kuma an kara wa’adin Makonni 6 ga wadanda ba su da katin zaman dan kasa daga 31 ga Disamba zuwa 9 ga Faburairu sabuwar shekara mai kamawa, da su gaggauta yin katin sannan su hada shi da layin su.
Wannan matakin ya zo ne bayan rahotanni da aka samu na irin yadda masu son yin rajistar katin zama dan kasa suka yi dandanzo a ofishin hukumar NIMC, dake Lagos domin ganin sun yi katin kafin cikar wa’adin da gwamnati ta diba na rufe layukan wayar da ba’a yi rijistar ta da katin dan kasa ba.
A nasa bangaren shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa ma’aikatar Sadarwa ta kasa game da sabon tsarin da ta bullo da shi na kokarin hada layin waya da katin zama dan kasa.
342/