10 Disamba 2020 - 14:21
Ghana : Nana Akufo Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

A Ghana, sakamakon wuin gani da hukumar zaben kasar ta sanar ya nuna cewa shugaban kasar mai ci Nana Akufo-Addo ne ya lashe zaben shugabancin kasar inda ya doke babban abokin takararsa tsohon Shugaba John Dramani Mahama.

ABNA24 : Sakamkon ya ce shugaba Akufo Addo karkashin jam’iyyar NPP, ya yi nasara da kashi 51,59 cikin 100 a yayin da shi kuma John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC ya samu kashi 47.36 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada yayin zaben na ranar Litini.

Saidai tuni babbar jam’iyyar adawa ta kasar NDC, ta ce za ta kalubalanci wannan sakamakon zaben.

Bayan ayyana shi dai a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar wanda aka sake zaba, Nana Akufo-Addo, ya nemi hadin kan ’yan kasar.

Ya ce, sakamakon babban zaben kasar, tamkar kira ne da ’yan kasar Ghana suka yi, game da bukatar manyan jam’iyyun siyasa biyu na kasar su yi aiki tare.

Shugaba Addo ya kuma baiwa ’yan kasar ta Ghana tabbacin cewa, zai yi aiki tukuru a wa’adi na biyu na shugabancinsu don inganta rayuwar jama’a.

Kafin hakan dai wakilai da masu sanya ido a zaben, sun bayyana gamsuwa da irin yadda aka kammala babban zaben kasar Ghana lami lafiya.

342/