Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakistan Zahir Hafeez Chaudhri yana fadar haka a birnin Islamabad a jiya Talata.
Chaudhri ya kara da cewa firai ministan kasar Imran Khan ya rika ya bayyana matsayin gwamnatin kasar dangane da haramtacciyar kasar Isra'ila (HKI) da kuma Falasdinu. Inda yake cewa matukar ba’a warware matsalar da ke tsakanin yahudawan da kuma Falasdinawa ba, ta yadda Faladinawa suka amince da abinda aka ba su ba, Pakistan za ta ci gaba da goyon bayan al-ummar Falasdinu ne.
Kafin haka dai kakafafen yada labarai da dama sun yada jita-jitan cewa gwamnatin kasar Pakistan za ta kulla huldar jakadanci da HKI bayan ziyarar da Natanyahu ya kai kasar Saudiya ya kuma gana da Muhammad bin Salman, wato yereima mai jiran gadon sarautar kasar. (19)
342/