17 Nuwamba 2020 - 13:46
An Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Yan Ta’adda 21 A Kasar Iraki

Majiyar jami’an tsaro a kasar Iraki ta bayyana cewa an zartar da hukuncin kisa kan ‘yan ta’adda wadanda aka dade da yanke masu hukuncin kisa saboda laifuffukan ayyukan ta’addanci da aka tabbata a kansu.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya ce an zartar da hukuncin kissan ne a babban gidan yari na Nasiriyya bayan da ofishin shugaban kasar ta Iraki ya amince da hukunce-hukuncen da ake yankewa yan ta’addan.

Tun bayan mamayar kasar Iraki wanda sojojin Amurka da Burtania suka yi a shekara ta 2003, dubban yan ta’adda, mafi yawansu yan kasar saudiya suka shigo kasar ta Iraki inda suka aiwatar da kashe-kashe masu yawa a kasar.

Wasu masana sun bayyana cewa yan ta’adda daga kasar Saudiya wadanda suka shiga kasar Iraki a wannan lokacin ya kai 15,000.

342/