15 Nuwamba 2020 - 14:31
​Iran A Shirye Take Ta Wadatar Da Kasar Iraki Da Makaman Da Take Bukata

Burgediya Janar Amir Khatami ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar a shirye take ta wadatar da kasar Iraqi da makaman da take bukata.

ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran ta nakalto Janar Khatami yana fadar haka a jiya Asabar a lokacin da yake ganawa da ministan tsaron kasar Iraki Jum’eh Enad Sa’adun wanda ya kawo ziyarar aiki a nan Tehran.

Khatami ya kara da cewa kasashen yankin yammacin Asia ne suka cancanci tabbatar da zaman lafiya a yankin nasu ba wasu daga waje ba.

Ministan ya kammala da cewa a duk lokacinda kasashen waje suka shiga yankin kudancin Asia su kan haddasa rashin zaman lafiya ne.

342/