ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ya nakalto majiyar sojojin na Siriya na cewa sojojin sun kaiwa mayakan ‘yan ta’addan farmaki ne a garin Jabal Zawiyya daga wajen birnin Idlib inda suka fatattaki da dama daga cikin su.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa farmakin ya hada har da kungiyar Tahrirusham wacce take rike da wani yanki a wajen birnin na Idlib.
Sojojin kasar ta Siriya suna ci gaba da fatattakar yan ta’aadar a wannan yankin, wanda shi kadai ne yan ta’adda suke iko da shi a halinyanzu a duk fadin kasar.
342/