29 Yuli 2016 - 10:19
Ci Gaba Da Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran A Wasu Kasashen Afrika

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana ci gaba da gudanar da ziyarar aiki a wasu kasashen yammacin Afrika, inda ya fara da Tarayyar Nigeriya, sannan Ghana, kuma a halin yanzu yana kasar Guinea Conakry, sannan zai kammala ziyarar da kasar Mali.

Tun a jijjifin ranar Lahadi ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarif da rakiyar tawagar 'yan kasuwa suka fara gudanar da wata ziyarar aiki a kasashen yammacin Afrika hudu inda suka fara da Tarayyar Nigeriya sannan Ghana, inda a halin yanzu suke kasar Guinea Conakry sannan zasu kammala ziyarar da kasar Mali.

A yayin ziyarar aikinsa a tarayyar Nigeriya ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarfi ya gana da mahukuntan kasar da suka hada da shugaban kasar da na Majalisar Dattijai da kuma ministan harkokin wajen Nigeriya, inda suka tattauna batutuwa da suka shafi hanyoyin karfafa alaka a tsakanin kasashen biyu tare da jaddada muhimmancin yaki da ta'addanci musamman kungiyar Boko Haram da halin yanzu take ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin Nigeriya da wasu kasashen makobtaka.

Bayan kammala ziyararsa a Tarayyar Nigeriya Muhammad Zarfi da tawagar da ke rufa masa baya sun nausa zuwa kasar Ghana, inda Zarif ya gana da shugaban kasar John Dramani Mahama kan hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu musamman harkar man fetur, gas, noma da harkar ilimi. sannan ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya gana da takwararsa na kasar Ghana Hanna Tetteh da kuma shugaban majalisar dokokin kasar, sannan ya kammala ziyararsa a kasar da gudanar da zama na musamman da Iraniyawa mazauna Ghana.

A jijjifin ranar Laraba ne ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya isa kasar Guinea Conakry inda a safiyar jiya Alhamis ya gana da shugaban kasar Alpha Conde kan hanyoyin bunkasa alakar siyasa da kasuwanci a tsakanin kasashensu, kamar yadda a zaman tattaunawansa da takwaransa na Guinea Conakry Mamadi Yula suka fi mai da hankali kan batun tattauna hanyoyin bunkasa harkar diflomasiyya da na tattalin arzikin kasashen biyu. Har ila yau a ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar Guinea Conarky sun jaddada aniyar kasashensu kan bunkasa harkar al'adu da na tarihi.

A bayan kammala ziyarar aiki a kasar Guinea Conakry; Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarif da tawagar da ke rufa masa baya zasu isa kasar Mali a yau Juma'a domin ganawa da mahukuntan kasar. Wannan ziyarar aiki da Muhammad Jawad Zarif ke gudanarwa a kasashen nahiyar Afrika yana matsayin shimfida ne na bude sabon shafi a fagen bunkasa harkar kasuwanci da na tattalin arziki a bangarori da dama tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen nahiyar Afrika. 288