24 Yuli 2016 - 04:44
Ana zaman makokin kashe mutane 80 a Afghanistan

Al'ummar Afghanistan na zaman makoki a ranar Lahadi bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai birnin Kabul ranar Asabar da ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 80.

Fiye da mutane 230 kuma sun samu raunuka a harin da aka kai cikin masu zanga-zanga 'yan kabilar Hazara marasa rinjaye, wadanda galibin su 'yan shi'a ne.

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai harin.

Shugaba Ashraf Ghani ya ce ya yi matukar bakin ciki da harin, inda ya sha alwashin daukar fansar mutanen da aka hallaka.

Ofishin MDD a Afghanistan ya bayyana harin a matsayin laifin yaki.

Wurin da akan kai harin bom din ya yi kace-kaca, kuma an bukaci jama'a su taimaka da jini.

Ma'aikatar cikin gida ta ce mutane uku ne su ka je da niyyar kai harin, amma daya ne kawai ya yi nasara.

Ma'aikatar ta ce bom din daya daga mutanen ya ki tashi a lokacin da ya ke kokarin kai harin, daya maharin kuma jami'an tsaro sun harbe shi.

Akwai mayakan kungiyar ta IS a gabashin Afghanistan, sai dai a baya, ba su taba daukan alhakin kai hare-hare a babban birnin kasar ba.288