A’uzu Billahi Minash Shaidanir Rajim.Bismillahir Rahmanir Raheem.Wasallallahu Ala Muhammadin Wa Alihid Dayyibinad Dahireen.
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuh.
An sani akan cewa muna cikin wannan watan ne na Sha’aban,kuma mun kai rabin shi kuma har mun wuce,kuma a rabin shi din ne aka haifi-a I’itiqadin mu –Al-Imamul Hujjah (afa).A wurin Malaman tarihi da nasabobi wadanda suke ba ‘yan shi’a ba wato ma’abuta fanni.Mun fadi a jalasosi a da cewa ko mun naqalto daga gare su akan cewa Al-Imamul Askariy (as) ya bar duniya ya bar da daya wanda ake ce mashi Muhammad.Sai su kan ce-wadannan Malaman dangantaku din da Malaman tarihi-shine wanda ‘yan shi’a suke raya cewa shine na sha biyu daga cikin limaman Ahlulbait.Wato kenan mun yi ittifaqi dasu a haihuwan shi,sannan mun bambamta a siffan shi dasu,saboda ne ya sa na ce a I’itiqadin mu lokacin ne aka haife shi(haihuwa da ma’anar IMAM).
Shi kamar yanda ruwayoyi suka fadi zai zo ne a karshen zamani ko kuma mu ce yace ya zo tun da labaran sun ambata akan cewa karshen zamani zai zo,to kuma ya haqqaqu tunda an haife shi a shekara 255 ko 256 hijra akan sabanin ruwayoyi.
Ya zo karshen zamani kuma shine wannan wanda Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya tanada domin haqqaqar da manufa wadda domin ita Allah Subhanu wa Ta’ala Ya halicci dan Adam,sannan kuma Ya sanya shi halifa a doron kasa.Shine yada adalci,ta yanda zai lullube dukkan ma’amura din gabaki daya,kuma adalcin ba zai tsaya akan yan Adan ba,zai zama ya shafi kowa da komai.Wadannan sanannun abubuwa ne ga dukkan mu ne abin kaddarawa,muna kaddara kowa da kowa ya san wannan cewa wannan shine dalilin da ya sa Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya tanaje shi.
Shi ba Annabi bane,amma Imam ne,kuma duk da haka Allah Subhanahu wa Ta’ala Yayi mashi wannan falala din ya zama cewa a hannun shi ne wannan manufa ta Allah Subhanahu wa Ta’ala zata tabbata kuma albarkacin kakan shi Manzon Allah (sawa) ya same shi.
Hakikanin al’amari ma shine wannan karshen zamanin,ta fara ne da haihuwar shi Manzon Allah(sawa).Ba ma da BI’ISA din shi ba(BI’ISA ta wuce a Rajab,27 ga shi a I’itiqadin mu).To karshen zamani da ake magana akai wanda a cikin shi ne wannan manufa zata haqqaqu,bai fara da haihuwar Al-Imamul Hujjah ba,ya fara ne da haihuwar Manzon Allah(sawa).Wato yanzu gaba daya muna cikin karshen zamani ne ko muna tsakiyar karshen zamani.Farkon karshen zamani din shine haihuwar Manzon Allah(sawa),shi kuma(Imamul Hujjah) zai zo a karshen karshen zamani ne.Mu muna tsakiyar farkon karshen zamani da kuma karshen karshen zamani.
Sakon da Manzon Allah (sawa) ya zo da shi shine sako na karshe kuma cika-maki kaman yanda yake shi Manzon Allah (sawa) shine Annabi kuma Manzo na karshe kuma cikamaki,shine AL-KHATAM ko AL-KHATIM kaman yanda suka ce akan sabani amma da MU’ADDA guda daya.Shine wanda ya rufe da ma’ana da yau da kullum da kuma ma’ana ta ma’ana da ma’ana da BADIN da ma’ana ta hakika wato da ma’ana yanda Malamai suke fadi cewa shine wanda ya cika dukkan martibobi na kamala.Kenan ba za a samu wata halitta-wannan in ya wuce har da mutum-daga cikin halittun da Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya halitta ba wadda zata iya kaiwa martiba ta kamala wadda zata kai Manzon Allah(sawa).KHATAMIYYA har da da wannan ma’anar wato SEAL da turanci.
Duk wata martiban kamala da mutum kan iya sawwalawa to Shi(Annabi) ya kai wurin kuma ya wuce,da ma’anar cewa a cikin halittun Allah Ta’ala gabaki daya ba samu wani wanda ya kai kaman Shi (sawa) ba a SHIDDA ta WUJUD wato asalin samuwa da afkuwa da tsananin tasiri a kusanci ga Allah Subhanahu wa Ta’ala wato kusanci MA’ANAWIY,wato a yin kama da Allah Subhanahu wa Ta’ala,wato shine mahalli na TAJALLIYAT na ASMA da SIFAT na Allah Subhanahu wa Ta’ala.Wannan shine ma’anar KHATAMIYYAH na Manzon Allah (sawa).
To! Al-Imamul Hujjah (as) shi kuma cigaba ne na wa’yannan kamaloli na Manzon Allah (sawa) ban da Annabci KAD’AN.Kenan,idan Manzon Allah (sawa) shine Al-Insanul Kamil kamar yanda suke cewa wato kenan dan Adam kammalalle,wannan wanda shine kalifan Allah,ba kowane dan Adam dan Adam ba.Lokacin da yake cewa INNI JA’ILUN FIL ARDI KHALIFATAN,to wannan wanda ya isa ya zama wannan khalifan Allah (sawa) shine irin wannan Al-Insanul Kamil din,ba kowane mutum mutum ba,wato wani mutum ne wanda yake kammalalle ne zai iya zama kalifa saboda kalifa ya kamata ya hiqaito maradodi da manufofi da da siffofi da dukkan MUWASAFAT din wanda yake halifta.
To idan Manzon Allah (sawa)ya kasance shine Al-Insanul Kamil kuma haka din ne shine Al-Insanul Kamil din,to Al-Imamul Hujjah (as) ya dauko wa’yannan siffofi na kamala na Manzon Allah (sawa) banda Annabci saboda haka a wannan zamanin shine Al-Insanul Kamil ko kace Al-Insan Al-Atam wanda mas’uliya din tafiyar da KAUN a madadin Allah saboda shine KILAFA din Allah Ta’ala wanda mas’uliyyar tafiyar da KAUN a madadin Allah ta doru akan shi.
A cikin AlKur’ani akwai isharori akalla mu ce wadanda suke nuni akan cewa haihuwan Manzon Allah (sawa) daga farko da kuma tayar da shi a Manzo a mataki na biyu,suna massala karshen zaman dan Adam a wannan duniya.Kaman misali Allah Subhanahu wa Ta’ala Yana cewa :
“ATA AMRULLAHI FALA TASTA’AJILUHU”ma’ana Al’amarin Allah ya zo-da sigan MADI,wato ya riga ya zo,al’amari Allah Yace ya zo saboda haka ka da kuyi gaggauta shi.
Malamai sun yi sharhin wannan ayan,kuma zamu yi ishara ya zuwa ga haka dan kadan.Kila in yi tanawulin wasu ayoyin,sannan sai mu zo mu ga yanda zasu dabbaqu akan maudu’in bahasin mu wanda shine Al-Imamul Hujjah(as).
A lokacin da Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya fadi wannan ayan,kuma a farkon ayan itace aya ta farko a cikin suran(an lura ai) Nahl.Kaman mun yi bincike a sashin suratun Nahl a tafsiran mu na shekaran da ta wuce.Lokacin da Yake cewa Allah Subhanahu wa Ta’ala :
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM,ATA AMRULLAHI FALA TASTA’AJILUHU SUBHANAHU WA TA’ALA AMMA YUSHRIKUN
A wurin sharhin riwayoyi na wannan ayan akwai abinda yake ishara ya zuwa wannan abin da na fada cewa zuwan Manzon Allah shine karshen zamani.
Allamah Tabataba’I kafin mu je wajen riwayoyin,a sashin tafsirin shin a ita ayan yana cewa:
DAGA NAN NE AKE IYA SANIN CEWA GINSHIKIN MANUFA A FARKON WANNAN AYAN SHINE BAYAR DA LABARI –wato abinda farkon suran nan yake so yayi-KARATOWAR AL’AMARIN ALLAH (ko mene ne wannan al’amarin na Allah)DA KUMA KUSANTUWAN SHI WANNAN AL’AMARIN ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA DIN YA ZUWA GARE SU,DA KUMA KUSANTAR SAUKAR SHI –tunda daga Allah zai zo sauka zai yi-AKAN SU (musamman Mushrikai),shi yasa yake cewa KUMA SHI WANNAN BADA LABARIN AKWAI NISANTAR WA DA KUMA KYECE DA GARGADI GA MUSHRIKAI,SABODA SUN KASANCE SUNA NEMAN A GAGGAUTO DASHI,WATO IN DA GASKE NE YA ZO AMMA SUNA YI NE DOMIN IZGILI DA NISANTARWA AKAN CEWA BA ZAI ZO BA SABODA BA SU YI IMANI DA ABIN DA YAKE FADA MASU DIN BA,TUNDA SUNA JI DA YAWA ALLAH TA’ALA YANA AMBATON SAUKAR AL’AMARIN SHI HAR SUNA CEWA YA KAWO SHI WATO YA ZO DASHI IN DA GASKE NE.To wannan yayi kama da fadin Allah a wata sura cikin Alkur’ani in da yake cewa:
“FA’AFU WASFAHU HATTA YA’ATIYALLAHU BI AMRIH”,ma’ana:Saboda haka kayi afuwa kuma kayi rangwame har sai Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya zo da al’amarin shi.To menene wannan al’amarin?Wannan ba wani abu bane face al’amarin shi Allah Ta’ala din na doruwar gaskiya akan karya,rinjayar gaskiya akan karya,da kuma bayyanar tauhidi akan shirka,da kuma bayyana da galabar imani akan kafirci.Wannan shine abinda tuntuntini a farkon surar yake iya baka ka gane.
Al’amarin Allah wani al’amari ne da in ya zo zai zama gaskiya ta bayyana karya ta tafi,sannan kuma tauhidi ya tabbata shirka sai ya zama imani ya haqqaqu kafirci ya tafi.
A lokacin da (Allamah Tabataba’i) ya zo yana bahasi na riwaya ya zo da abubuwan da suke ishara zuwa ga wannan abin da muke bayani akai.Kaman akwai shi a cikin tafsirin Ayyashi daga Hisham Ibn Salim daga sashin sahabban mu daga Al-Imamus Sadiq (as) yake cewa NA TAMBAYI SHI DANGANE DA FADIN ALLAH TA’ALA “ATA AMRULLAHI FALA TASTA’AJILUH”,SAI IMAM SADIQ YACE IDAN ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA YA LABARTA MA ANNABI (SAWA) DA WANI ABUN DA ZAI AUKU ZUWA WANI LOKACI,TO SHINE FADIN ALLAH TA’ALA “ATA AMRULLAH FALA TASTA’AJILUH”WATO AL’AMARIN ALLAH YA ZO SABODA HAKA KA DA KU GAGGAUTO DASHI-wato kenan ya auku la mahala.Idan Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya labarta ma Manzon Shi cewa kaza zai faru a wani lokaci a gaba,me yake nufi kenan?Wannan abun MUTAHAQQIQ NE ko GAIRU MUTAHAQQIQ?abu ne wanda yake MUTAHAQQIQ JAZMAN wato zai faru jazman kuma kome ne wannan al’amarin.Wato YATAHAQQAQU LA MAHALA,saboda haka ba amfanin ka gaggauto dashi,kace dole kana so ka ganshi yanzu,zai faru ka jira-
(riwayar ta cigaba )SABODA HAKA KA DA KU GAGGAUTA SHI HAR SAI WANNAN LOKACIN YA ZO.
Sai kuma riwaya ta biyu,Imam Sadiq yace:SHI ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA IDAN YA BADA LABARIN CEWA WANI ABU ZAI KASANCE KAMAN KAI KACE YA KASANCE NE-shi yasa Allah Ta’ala idan yana bada labarin ranar Alkiyama,yana bada labarin wuta da aljanna yana bada labarin akan sun faru ne.In ka je Alkur’ani zaka ga Allah na baka labarin ‘yan wuta a cikin wuta da ‘yan aljanna a cikin aljanna saboda a wurin Allah wadannan abubuwan sun riga sun faru kaman ana gangara lokacin ne zuwa ga faruwan wannan abin,to sun faru.To lokacin da Allah Yace “ATA AMRULLAH “ al’amarin Allah ya zo,to ya riga ya zo kawai ana jiran lokacin shi ne ya afku.
Ba zaka kawo ishkal ba kace to me yasa tun daga lokacin da Allah Ya fadi har yanzu bamu gani ba,sai muce maka INTAZIR wato saurara zai faru,shi yasa muka ce farkon haihuwan Manzon Allah (sawa) shine farkon faruwan wannan “AMRULLAH”.
Sannan sai Al-Allamah Tabataba’I yake cewa:sai ni kuma nake cewa,kaman kai kace ishara a cikin ta’abirin da akai a ayan da lafazin MADIY (da yace ATA ba YA’ATIY ba,al’amarin Allah ya zo )ka man kai kace ya faru ne ko afkuwan al’amarin ne LA MAHALA.Idan Allah Ta’ala Yace abu zai faru to zai faru ne.Da Yace Sahibuz Zaman za a haife shi –da yace harshen Amintattu-ga inda zai kasance,ka man ya riga ya faru ne,shakkan mai shakka,shubhan mai shubha,ishkal din mai ishkal,izgilin mai izgili wa’yannnan basa canja kome kuma basa jirkitarwa,shi kawai ake jira.Izgilin bai sawa ya matso sannan bai sawa ya jinkirta sannan ba zai hana shi ya zo ba,wato zai faru kad’an alhali mutum bai shirya ba.
Ya zo a cikin Al-Durrul Mansur na Al-Allamah Suyudi,yana cewa:Ibn Mardawiy ya fitar cewa a lokacin da Allah Ya saukar da wannan ayan “ATA AMRULLAH….”sai Sahabban Manzon Allah (sawa)suka kideme suka gigece (saboda fahimtar su da larabci da sanin ma’anar abinda ayan take nufi)suka firfito daga cikin gidajen su suna ganin kaman kiyama ta riga ta tsaya har sai da FALA TASTA’AJILUH wato ka da ku gaggauto shi ta sauka suka fahimci wannan,to a lokacin sai suka natsu,sun san cewa anan gaba ne amma yanzu ne.Da muka ce wannan karshen zamani ne haka muke nufi ya zo wato ATA AMRULLAH al’amarin Allah ya zo haihuwan Manzon Allah(sawa).
Akwai riwayoyi irin wadannan wanda ban da lokacin kawo su sannan ban so in dade a cikin su.Tabarani ya rawaito daga Asaba bn Amir kuma AlHakim ya inganta riwayar,yana cewa:Manzon Allah Sallalahu alaihi wa Alihi wa Sallam yace kafin sa’a wato alkiyama abinda zai bijiro maku akwai wata girgije baki daga fuskacin yamma,sannan wannan girgijen ba zai gushe ba yana karuwa har sai sama ta cika sai mai kira yayi kira yace “Ya ku mutane”sai wani sashin mutane ya fuskanci wani sashi su ce kun ji abinda muka ji kuwa,a cikin su akwai masu cewa sun ji akwai masu shakka,sannan sai mai kiran ya kara kiran na biyu yana cewa Ya ku mutane,sai wasu mutane su ce to kun ji?sai kowa yace ya ji.Sai mai kira ya kara kira yace ATA AMRULLAHI FATA TASTA’AJILUH……A lokacin sai Manzon Allah Yace Na rantse da wanda rai na ke hannunsa zaka samu mutane guda biyu a lokacin da aka yi wannan kiran sun shinfida mayafi zasu ci abinci ko wani abu amma ba zasu iya nannade shi (wato lokaci ya riga yayi),sannan hakika mutum zai cika komin shi domin kila dabbobi su sha amma sai ya zama bai iya shayar dasu saboda tsayuwar sa’a,kuma hakika mutum zai tatsi taguwar shi domin ya sha madara amma sai ya zama ba lokaci da zai sha madara din…har zuwa karshen abinda Al-Allamah ya fadi anan gun
24 Yuli 2016 - 04:38
Lambar labari: 767580
JAWABIN SHEIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL NA NISFUSH SHA’ABAN 2016 YUSUF SULAIMAN NE YA RUBUTA.