27 Yuni 2016 - 13:40
Avengers na son Buhari ya ziyarci Niger Delta

Kungiyar Niger Delta Avengers sun bukaci Buhari ya ziyarci yankinsu don ganewa idonsa halin da yankin ke ciki

Kungiyar Avengers da ke yankin Niger Delta a Najeriya wadda a watannin baya-bayan nan ta sha daukar alhakin kai hare-hare akan bututun mai, ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya kai ziyara a yankin.

A sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ce lokaci ya yi da ya kamata Buhari ya ziyarci yankin domin ganewa idanunsa yanayin da gwamnatoci da kuma kamfanonin mai suka jefa jama’a.

A cikin watan jiya, shugaban ya bayyana aniyarsa ta kai ziyara a yankin, kafin daga bisani a soke saboda wasu dalilai.288