Kamfanin dillancin labaran Sepah News ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya ne dakarun kare juyin juya halin suka yi artabu da 'yan ta'adda a yankin Mahabad da ke cikin lardin Azarbaijan da ke yammacin kasar.
Rahoton ya ce an halaka wasu daga cikin 'yan ta'addan yayin musayar wuta, an kuma damke wasu da makaman da ke hannunsu, rundunar ba ta yi karin haske kan mutanen da kuma inda suka fito ba.
A farkon wannan makon dakarun kundumbala na rundunar tsaro ta musamman a kasar Iran ta sanar da cafke wasu 'yan ta'addan da suke shirin kaddamar da hare-haren bama-bamai a wurare 50 da suka hada har da cikin birnin Tehran, wadanda suke da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS, kuma sun bayyana kasashen Amurka da Saudiyya a matsayin masu daukar nauyinsu domin aiwatar da wadannan ayyuka na ta'addanci a cikin kasar Iran.288