Miliyouin Iraniyawa suna suna gudanar da makokin rasuwar Imam Khomani (q) wanda ya assasa Jumhuriyar Musulunci ta Iran shekaru 37 da suka gabata.
A nan birnin Tehran ana saran miliyoyin masoyan Imam daga ciki da wajen kasar ne zasu halarci makokin da za'a gudanar a humbarensa mai tsarki a nan kudancin Tehran. Ana saran Jagoran juyin juya halin Musulunci Aya . Sayyeed Aliyul Khaminae zai gabatar da jawabi nan gaba kadan a cikin haraminsa.
An haifi Marigayi Imam Khomani (q) a garin Khumain a nan Tsakiyar kasar Iran ya tashi a gidan malamai, ya kuma fara gwagwarmaya da sarakunan Palawi a kasar ne a shekara 1963, sannan ya yi gudun hijira na tsawon shekaru 15 a kasashen waje, sannan ya dawo a ranar 1-Febrerun-1979 inda ja kammala jagorancin juyin juya halin zuwa ga nasara. Ya kuma jagoranceta na tsawon shekarum 10 sannan ya rasu yana dan shekara 87 a duniya a ranar 3-Jyuin-1989M.