A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Tunusiya ta fitar a yau Laraba yana dauke da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar gano wasu gungun 'yan ta'adda a lardin Mahdiyya da ke kudancin kasar ta Tunusiya, inda suka kai farmaki tare da samun nasarar kame 'yan ta'addan.
Gungun 'yan ta'addan sun yi furuci da cewar suna aiki ne karkashin kungiyar ta'addanci ta Da'ish kuma ayyukansu sun takaita ne a fagen sada zumunta da nufin gurbata tunanin matasa.288