Dimbin 'yan uwa maza da mata ne suka sami damar halartan wannan buki da aka gabatar da tun da safe zuwa yamma a makarantar Fudiyyah cikin birnin Zariya.
Malaman da suka gabatar da jawabi a lokacin wannan gagarumin buki sun hada da Malam Kabir Malumfashi, Malam Ibrahim Akil, da kuma Malam Muhammad Abbare.
Tun kafin nan kuma da safe Malamai da suka hada da Malama Maimuna Hussain da wasu 'yan uwa mata sun gabatar da jawabai daban daban.
'Yan makarantar Fudiyyah da suka hada da Primary da gaba da Primary suma ba'a bar su a baya ba a wajen halartan wannan gagarumin buki.
Bayan an kammala gabatar da jawabai ne daga karshe aka gabatar da yanka Alkaki don girmamawa ga Sayyidah Zahra[SA] wanda Malam Ibrahim Akil ya yanka, sannan sai aka mayar da abin Magana ga Malam Sunusi Abdulkadir daga Kano wanda ya rufe taron da addu'ah.
Bayan an kammala taron ne kuma mahalarta suka gabatar da muzahara, suna kiran a gaggauta sakin Malam[H], da sauran dukkanin 'yan uwa dake tsare a gidajen kaso.
An dai kammala taron lafiya kuma mahalarta sun kama hanyar komawa gidajen su.288