27 Maris 2016 - 17:22
Putin Da Hukumar UNESCO Sun Jinjinawa Sojojin Syria Saboda Kwato Palmyra Daga Hannun ISIS

Cibiyoyi na kasa da kasa da shugabanni da 'yan siyasa na kasashe daban-daban suna ci gaba da nuna farin cikinsu da kuma taya gwamnatin kasar Siriya murnar nasarar da sojojin kasar suka samu na kwace birnin Palmyra mai tsoho tarihi daga hannu 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS).

Babbar daraktar Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kayan Tarihi (UNESCO) Irina Georgieva Bokova, cikin wata sanarwa da ta fitar, ta nuna farin cikinta da kuma jinjinawa sojojin Siriyan saboda nasarar da suka samu na fatattakan 'yan ta'addan daga garin.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da takwararsa na kasar Siriyan Basshar al-Asad, ya taya shugaban Siriyan murnar nasarar da sojojin nasa suka samu na kwato garin na Palmyra yana mai jaddada wajibcin ci gaba da kiyaye kayayyakin tarihi na birnin. Shi ma a nasa bangaren shugaba Asad ya bayyanar godiyarsa ga irin taimako da goyon bayan da gwamnatin Rashan take ba wa kasar Siriyan a fadar da take yi da 'yan ta'adda.

A yau ne dai kafafen watsa labaran kasar Siriyan suka sanar da kwace garin na Palmyra daga hannun 'yan ta'addan ISIS din bayan gumurzu na kwanaki tsakanin 'yan ta'addan da sojojin Siriyan wadanda suke samun goyon bayan dakarun kungiyar Hizbullah. Gidan talabijin din kasar Siriyan ya bayyana cewar sojojin sun sami nasarar kwance bama-bamai da nakiyoyi da 'yan ta'addan suka daddasu bugu da kari kan wasu makamai masu linzami da aka samu a filin jirgin saman garin da 'yan ta'addan suka gudu suka barsu.

Kungiyar Da'esh ta kama birnin Palmyra ne a watan Mayu na shekara 2015 inda suka lalata wasu daga cikin kayayyakin tarihi na birnin.288